KASAR ANGOLA TA HARAMTA MUSULUNCI Kasar angola ta zama kasa ta - TopicsExpress



          

KASAR ANGOLA TA HARAMTA MUSULUNCI Kasar angola ta zama kasa ta farko a duniya data fito ta bayyana cewa ba a yarda ayi addinin musulinci ba a cikin kasar, kuma gwamanati ta bada umarni rushe wasu masallatai wasu kuma tace a rufe su. Ita dai kasar Angola tana kudancin nahiyar mu ta Afirka ne, kuma tana makwabtaka da Congo kinshasa da Congo Brazabil da Namibia. Sannan a kiyasi kasar tana da yawan mutane milyan 18 kuma an kiyasta yawan musulmai bai wuce mutum dubu 80 zuwa 90 ba. Amma duk da haka gwamnati ta hukunta cewar in mutum yana son yin addinin Islama sai dai ya fice ya bar kasar. Da wannan muke rokon Allah, dan kudurarka dan buwayar ka, dan izzarka dan karfin mulkinka, Allah ka hana wannan kasa wanzuwa kamar yadda suke kokarin hana haskenka (islam) wanzuwa a cikin kasar. Ameen
Posted on: Sun, 24 Nov 2013 19:45:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015