KO AKWAI DARASI A CIKIN WANNAN LABARIN ??? ================ Wata - TopicsExpress



          

KO AKWAI DARASI A CIKIN WANNAN LABARIN ??? ================ Wata rana wani Malami cikin malamai yana koyar da dalibansa akida (tauheed) ana magana akan LÃILÃHA ILLALLAH yana tayi musu bayani a kanta sharuddanta da kaidodinta. Yana tarbiyantar dasu akanta, ana cikin haka wata rana sai wata daliba ta kawowa malamin nasu kyautar tsuntsun AKU gashi malamin dama yanason kiwon tsintsaye da dabbobi, sai yazama duk lokacin da malamin zaije yayi musu karatu yana fita da wannan AKUN. Yauda gobe har AKU ta iya fadin LAA ILAAHA ILLALLAH. kuma tana yawaita fadin kalmar dare da rana, kawai wata rana sai daliban suka sami malamin nasu yana kuka sosai! Sai suka tambaye shi komene yasa kake kuka? malam yace: Ai kyanwace (mage) ta kashemin AKU!. Sukace masa yadaina kuka indan wannanne zasu kawo masa wata AKUN wacce tafi waccan. sai malamin yace: badan haka nake kukaba, aa ina kukane saboda lokacin da kyanwar zata kashe AKUN sai akun take ta kuka, (kara), ta manta da kalmar LAA ILAAHA ILLALLAAH! saboda ita (AKU) tasan kalmar abakine kawai bata santa a zuciyaba saboda haka nake kuka, inajin tsoron kada MUTUWA tazomin namanta da kalmar. LAA ILAAHA ILLALLAH! kamar yadda AKU ta manta da ita. Sai daliban suma suka kama kuka tareda malamin nasu! * * Ya Allah ka azurtamu da kalmar LAA ILAHA ILLALLAHU a yayin mutuwarmu.! Dan Allah kuce AMEEN Daga. ↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓↓ HAMEES ALHAMEES ¤==¤ ¤==¤ ¤==¤ HHHHHHHH 2gousername hamisalhami
Posted on: Sat, 23 Nov 2013 05:14:36 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015