KU KARANTA KUJI IRIN WULAKANCI DA CIN AMANAH Na gama komai - TopicsExpress



          

KU KARANTA KUJI IRIN WULAKANCI DA CIN AMANAH Na gama komai na aladar mijina kafin ya kwanta sai na koma dakina Dan na kintsa in dawo dan raya wannan dare, sai kyalli da kamshi nake na san hubbyna zai yaba kuma zai gigice in har ya shaki kamshin jikina,na shiga da sallamata da faraata da zumudi sai dai kash baya sitting room Kamar yadda na barshi sai na doshi bedroom..... nayi takaici nayi bakin cikin abunda kunnuwana suka jiyo min.Mijina naji yana Waya ga abunda yake cewa: No baby kinsan INA sonki INA kaunarki kedai ki kara hakuri Kamar yadda nace miki, sai naji shiru da kamar in koma sai kuma naji yace Pls ba haka bane kinsan ba macen da nakeso nake kuma jin dadinta kamarki kai muryarki kadai idan naji sai hankalina ya tashi, a hankali na karaso cikin dakin take naji Wani Abu ya tokareni a wuya na hadiyeshi da kyar. Sai na koma da baya na jingina da bango sai naji yana cewa ki bari zan shirya mana tafiya ta oneweek ai dama bamu gama honeymoon dinmu ba kawai Dan bana son ta gane ne na dawo gida. ki shirya gobe 7:00 na safe Muna tare. Na kusa suma da kyar na daidaita kaina wai mijina aure yayi ban sani ba kuma Ashe baya jin dadina na dai daure nayi sallama da karfi na shigo sai ya canza zancen OK gobe 7:30 ne meeting din as early as 7 zan shigo Insha Allah, OK saida safe OK nima haka. Yana juyowa sai ya cemin min matata abun alfaharina mai kika tsaya yine kika barni da jira da kewa? Ya kalleni na danyi yake, ya ce kai wannan kwalliyar fa ta daukan hankali ya bude min hannu wai in taho ban mu sa ba dan na matsu inji karshen rainin hankalin ne sai naji yana radamin a kunne farin ciki na gobe in Allah ya kaimu zan fita da wuri Dan muna da meeting ba mamaki ma mu tafi abuja workshop na 0neweek ban dai San yadda zata kasanceba kidai shirya min kayana should incase. Toh Yan Uwa Idan kune Wane mataki zaku Dauka??
Posted on: Mon, 02 Dec 2013 21:31:39 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015