•KUKAN KURCIYA GA JONATHAN• Tazarcen Jonathan A Tarin Yajin - TopicsExpress



          

•KUKAN KURCIYA GA JONATHAN• Tazarcen Jonathan A Tarin Yajin Aikin Ma’aikata. Masana kan kimiyyar siyasa irin su shahararren malamin jami’ar nan ta Amadu Bello da ke Zariya, marigayi Dakta Bala Usman, a cikin rubuce-rubacensa da dama ya yi nuni da cewa, babban ma’aunin da ke bayyana salon shugabanci a kasa na kan tirba shi ne ta yadda ‘yan kasar ke nuna goyon bayan su ga shi musanman ta hanyar yadda kungiyoyi sa-kai da na ma’aikata wadanda su ne wakilan al’umma suka rungumi tafiyar sa. Ya zuwa yanzu dai a iya cewa, gwamnatin Shugaba Jonathan na tafiya ne a bisa doron tarin yajin aikin kungiyoyin ma’aikata da dama da suka hada da kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta kasa wato ASUP wanda a yanzu sun kwashe kimanin watanni biyu suna yi babu alamun daidaitawa, duk kuma da kiraye-kirayen da daliban wadannan makarantu suke ta yi na cewa sun gaji da zaman kashe wando a gidajen su. Bayan wannan akwai kungiyar malaman makarantun firamare wanda su ma suke neman karin kashi 27.5 a kan albashin su, wanda bai wuce dubu biyu zuwa dubu uku ba ga karamin malamin da albashin sa bai wuce dubu goma sha uku a jihohin da suke koyarwa, koda yake wannan alhakin gwamnoni ne. Batun karatun firamare da kuma karin albashin da kungiyar malaman ta NUT suke nema, duk da irin masifar da wannan yajin aiki zai haifar ga harkar karatun yara a firamare wacce ita ce cibiyar dashen kowane ilimi amma gwamnatin tarayya ta yi kememe ta ki saka baki domin warware wannan yajin aiki wanda kusan ya wuce wata daya yanzu a wasu jihohi, hakan kuma ya sa kananan yara ‘yan firamare ci gaba da wantagaririya a manyan titu¬nan biranen kasar suna tallar ruwan sha na leda. Haka kuma na baya bayan su ne, kungiyar masu aikin hako danyan mai fetur da suka shiga nasu na kwana uku a matsayin jan kunne domin biya musu bukatun su na alkawarin karin alawus da ta yi musu, matsayin kuma da tuni ya haifar da karancin man fetur da jerin gwanon motoci a gidajen mai musanman a manyan burine kamar, Kano da Abuja da Legas da Fatakwal ta jihar Rivers kuma hakan na iya sake jefa talaka cikin mawuyacin hali. Bayan haka ita ma, babbar kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa wato ASU, an wayi gari tashare kusan wata 4 dashiga yajin aikin sai baba ta gani domin tursasawa gwamnati ta ciki musu alkawarin da ta dauka na ba su karin alawus-alawus na, wanda kuma jami’an gwamnatin ta sha yin alk-awrin cewar ta ware wasu makudan kudade domin warware wannan matsala amma dai har yanzu babu alama. Wani babban abin takaici ga wadannan jerin zanga-zanga aiki da ta kewaye bakin gwamnatin kusan na iya haifar da rudani ga tafiyar harkokin mulki a kasar da ma ita kanta gwamnatin baki daya ganin idan aka kwatanta da irin abubuwan da ke faruwa yanzu a Gabas ta Tsakiya inda karamar zanga-zanga kan haifar da kifewar gwamnati baki daya. Bayan haka wani babban abin takaici a halin da ake ciki wannan tarin yajin aiki shi ne, na yadda shugaban ya karkata akalar shugabancin kasar baki daya ga rigingimun da ke damun jam’iyyarsa ta PDP da wasu gwamnonin maimakon sanya ido kan al’amurran da suka shafi ma’aikatan da ke tafiyar da hukumomi ko cibiyoyin gwamnatin da ke fafitikar kyautata rayuwar al’ummar kasar da ke fama da ukuba a yanzu ta fatara da talauci da rashin tsaro da rashin aikin yi, musanman a tsakanin kimanin matasa miliyan arba’in da ke warwatse a jihohi daban-daban na kasar nan. A saboda ya kusa babban aikin da ke gaban gwamnatin Shugaba Jona-than a yanzu shi ne na kokarin samo bakin zaren warware wadannan yajin aiki da ya nufi gwamnatin gadan-gadan kafin ya watsu ya zuwa wasu sassan ma’aikatun gwamantin da su ma suke wasa wukaken su a yanzu. GYARA KAYANKA??
Posted on: Sat, 19 Oct 2013 23:36:47 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015