KUSUFEWAR RANA: Ko Ya Yanayin Ya Kasance A Yankunanku?Daraktan - TopicsExpress



          

KUSUFEWAR RANA: Ko Ya Yanayin Ya Kasance A Yankunanku?Daraktan cibiyar biknciken sararin samaniya na jamiar Nijeriya dake Nsukka, Farfesa Fidelis Opara ya bayyana lokutan da ake tsammanin kusufewar rana a yau zai kasance a yankuna daban daban na kasar nan.Kamar yadda Farfesa Opara ya bayyana kusufin zai kasance kamar haka: a Abakaliki tsakanin 1.06pm zuwa 4.09pm, a Ibadan tsakanin 12.52pm zuwa 4.01pm, a Port Harcourt tsakanin 1.03pm zuwa 4.09pm, a Enugu tsakanin 1.04pm da 4.07pm, a Lagos tsakanin 12.50pm 4.01pm, a Kano tsakanin 1.07pm zuwa 4.01pm; a Abuja tsakanin 1.03pm zuwa 4.03pm sai kuma a Uyo tsakanin 1.06pm zuwa 4.09pm.Sannan ya kuma bayyana cewa sauran wuraren da kusufin zai shafaa kasashen duniya sun hada da: biranen Hamilton, Bermuda, New York, New York na Amurka, sai biranen Freetown, Sierra Leone, Monrovia, Liberia; São Tomé, Sao Tome da Principe; Malabo, Equatorial Guinea; Port-Gentil, Gabon; ibreville, Gabon; Yaoundé, Cameroon; Brazzaville, Congo; Kinshasa, Congo Dem. Rep; Bangui, Central African Republic; Juba, South Sudan; Kigali, Rwanda; Kampala, Uganda; Addis Ababa, Ethiopia; Nairobi, Kenya da Mogadishu, Somalia.Zuwa yanzu mun tuntubi wakilanmua wasu jihohi inda wasu suka bayyana mana cewa abin bai fara faruwa a jihohin da suke ba, sai dai wasu sun bayyana cewa abin ya fara faruwa kadan - kadan, jihohin sun hada da Lagos, Kaduna, Kano, Gombe.Shin ya yanayin kusufewar ranar yake a jihohinku?
Posted on: Sun, 03 Nov 2013 16:08:40 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015