LABARI: Jonathan Ya Yi Ganawar Sirrin Da Sule Lamido Da Babangida - TopicsExpress



          

LABARI: Jonathan Ya Yi Ganawar Sirrin Da Sule Lamido Da Babangida Aliyu Shugaban Goodluck Jonathan a daren jiya ya yi wata ganawa da gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da takwaransa na jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu, wadanda suka bayyana zaman su a PDP bayan da bangaren sabuwar PDP ya bayyana hade da jamiyyar adawa ta APC. Tun da farko kafin fara ganawar ta su, Jonathan din sai da ya yi wani zaman na daban da gwamnonin jamiyyar ta PDP, duk a fadar ta shugaban kasa, wanda mataimakin shugaban kasa, Arch. Namadi Sambo da sakataren gwamnatin tarayya, Pius Anyim, duk suka halarta. Sai dai sakamakon hana shigar yan jaridu, har yanzu ba a san musabbabin ganawar gwamnonin da shugaban kasar da mukarrabansa ba, wadda aka yi ta da misalin 7:30 na dare zuwa 8:40. Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da: Emmanuel Uduaghan (Delta), Theodore Orji (Abia), Isa Yuguda (Bauchi), Jonah Jang (Plateau), Ibrahim Shema (Katsina), Seriake Dickson (Bayelsa) Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Martins Elechi (Ebonyi), Sullivan Chime (Enugu), Idris Wada (Kogi), da kuma Liyel Imoke (Cross River). Ya yin da gwamnonin Neja da Kaduna suka tura mataimakansu su wakilce su. Bayan kammala zaman da gwamnonin, sai kuma aka shiga ganawar sirri, tsakanin shugaban da gwamnonin Neja da na Jigawa, a dakin taro na First Lady dake fadar ta Villa. Har zuwa wannan lokaci dai ba mu samu sakamakon matsayar da aka cimma a ganawar ba, wadda gwamnonin suka ce ita ce za ta ba su damar shiga jamiyyar APC ko ci gaba da zaman su a PDPn. An dai aika wa sauran gwamnoni biyar din da suke bangaren sabuwar PDP kafin hadewarsu da APC takardar gayyata, sai dai cikin su babu wanda ya amsa gayyatar. Ko a jiya ma dai gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, bayyana cewa ya yi, daga yanzu duk lokacin da zai halarci wata ganawa da Jonathan zai yi ne a matsayinsa na gwamnan APC ba na PDP ba.
Posted on: Mon, 02 Dec 2013 06:37:00 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015