LABARI: PDP Ta Yi Allah-wadai Da Kokarin APC Na Janyo - TopicsExpress



          

LABARI: PDP Ta Yi Allah-wadai Da Kokarin APC Na Janyo G-7 Jamiyyar PDP mai mulki ta yi Allah-wadai da kokarin da APC take yi na son janyo hankalin gwamnonin da suka balle daga jamiyyar su bakwai wato G-7, zuwa cikinta. A cewar PDP, APC munafukar jamiyya ce wadda ba ta da wata kwakkwaran manufa, kamar yadda sakataren yada labaranta Olisa Metuh ya bayyana cikin wani jawabi da ya fitar a ofishin jamiyyar a yau a Abuja. Jamiyyar ta kara da cewa kokarin janyo gwamnonin da APC take neman yi ba zai taba ja mata da mai ido ba. Abu ne a zahiri cewa APC taron munafukai ne da yan gudun hijirar da ba su da wata manufa illa su mulki Nijeriya ko ta halin kaka, sai da abinda suka manta shi ne yan Nijeriya ba wawaye ba ne, sannan ba za su bari a yaudare su ba a cewar jawabin na PDP. Sannan PDP ta tabbatar da cewa babu wani halastaccen danta da zai fita ya koma APC. Haka ta kuma ta zargi APC a matsayin jamiyyar masu tsattsauran raayin addini da suke goyon bayan rikice - rikicen addini da na kabilancin da yake faruwa a kasar nan. Shiga cikin APC kamar goyon bayan tashe - tashen hankulan kasar nan ne, da goyon bayan barayin shugabanni irin su Asiwaju Bola Tinubu wanda ya maida Lagos da wasu jihohin Kudu-maso- Yamma tamkar gidansa, wanda a yanzu ba shi da aiki sai tursasa gwamnonin jihohin suna sace dukiyar jamaa tana zama ta su, da matsawa jamaa kan biyan haraji mai yawa don su kawata rayuwarsu marar amfani in ji Mista Olisa. Sannan a karshe ya yabawa shugaba Goodluck Jonathan kan juriya da hakurin da yake yi kan duk wani farmaki da yan adawa suka ke kawo masa, saboda haka ya nemi yan Nijeriya su ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa da ajendarta ta kawo ci gaba, wanda ya ce zai amfanar da kowa.
Posted on: Thu, 31 Oct 2013 18:02:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015