LADABIN BIYAN - TopicsExpress



          

LADABIN BIYAN BUKATA ◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇ Allah mai iko,Addini dan sauki. Wato in dai Addinin Musulunci ne yazo mana da yadda zamuyi komai,sai dai ko mune bamu fahimta ba. Shi ladabi ba iya Iyaye,Malamai da mutanen Unguwa ake yiwaba,saboda gashi har na biyan bukata da akwai. Da farko idan mutum zai biya bukata a bandaki dole zai bi matakai kamar haka: ①Zai fara sa kafar hagu. ②Sannan yayi Adduar da Annabi ya tanadar yayin shiga Bandaki ③In an shiga bandaki Baa yin waka. ④Kuma baayin Magana da wanda ke waje. ⑤Kada ka fuskanci gabas. ⑥kuma kada ka Ambaci Allah,ko kayi karatun Qurani,domin baa ambatan Allah a wajan Najasa. ⑦yin Adduar fitowa daga bandaki.. #Admin by: Jalaludden Muhd Abdulkadir
Posted on: Tue, 19 Nov 2013 21:40:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015