LANCIN DIN SU JINGIR BABU RIBA SAI FADUWA - TopicsExpress



          

LANCIN DIN SU JINGIR BABU RIBA SAI FADUWA (2) *********************************** 4. In baku manta ba ai bara ma anyi wannan taron lancin din kuma in aka yi laakari da wancan zaka tabbatar da rashin nasarar wannan din, misali a wancan lokacin muna tafiya tare mataimakin shugaban kasa yazo, gwamnoni hudu sun zo mataimakan gwamnoni biyu sunzo sarkin musulmi yazo shehun Borno ba a maganar wakilan gwamnoni dana sarakuna yan majalisu kuwa da ministoci ba iyaka yanzu kuwa babban makaryacin nan ne gomnan Neja sai kakakin majalisar wakilai suka samu halarta wanda hakan ya nuna ashe duk dalilin mu suka zo. Shi yasa bana da muka ce mun daina lancin sai suma suka ce suma sun daina zuwa lancin. ***jamaa ya kamata mu rika jin tsoron Allah in mutum bai fahimci magana ba ya daina dorarwa a update da nayi na baya babu inda nace Jingir ne ya kashe bayin Allahn da suka riga mu gidan gaskiya ku kara komawa ku karanta post din da kyau. Abinda na fada shine Jingir yayi sanadiyyar mutuwar su. Duk masanin harkar sharia (law) ya san abinda nake nufi. Ni ba jahili bane kuma banyi rubutu na cikin jahilci ba. Na farko dai a kaida duba variation and rule of compensation zaka san cewa a kaida duk wanda ka nemi kudi dashi maana kayi amfani dashi ka samu kudi to duk tsautsayin da ya same su, suna da diyya a kanka. In za ayi amfani da dokokin federal employment compensation act zamu fahimci cewar lallai Jingir shi yake da hakkin biyan kudin diyya don kuwa yayi amfani dasu gurin neman kudi ne. Don illahirin taron lancin din baka isa ka kira shi waazi ba don kuwa sai malami ya hau ya sauka bai ja aya ko sau daya ba saidai kawai fadanci da nunawa kakakin majalisa da talban minna cewa wadannan duk talakawan ku ne suka taru. Kuma kamar yadda na fada da ace iyalan mamatan zasu nemi hakkin su, ba shakka zasu samu, dan kaset din lancin din kawai zasu kai kotu a matsayin hujja cewar an fake da waazin kasa an nemi kudi da yan uwan su, kuma tabbas kotu zata ga yadda shi kansa Jingir bai yi karatu ba daya hau minbari illa neman gyara miya. Ni dai kawai fata na shine yan uwa su tashi su nemi ilmi karsu tsaya duhun kai yayi musu kanta abu mai sauki ya rika daure musu kai kuma abin bakin ciki sai kaga mutum bai ma san meye hakkin sa ba
Posted on: Fri, 31 Jan 2014 22:30:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015