# MABARUKAH (1) Daga Jameel Ameenu Journalist A kofar katon - TopicsExpress



          

# MABARUKAH (1) Daga Jameel Ameenu Journalist A kofar katon asibitin taja ta tsaya da motar ta,wanda yake amsa sunansa da NORTHWESTERN MEMORIAL HOSPITAL.Wannan shine na uku ta na zuwa gurin likitan mahaifin nata dr Dowson domin biyan wata bukatar ta,amma likitan yaki amincewa da bukatar tata.saboda haka wannan zuwan datayi shine nakarshe ta ayyna acikin zuciyarta,lallaine ko dr dowson naso ko baya so dole ne yau ya yarda da abinda take son yayi mata. Kai tsaye office dinsa tanufa,kuma babu wata alama ta murmushi ko sakin fuska a tare da ita. Shi kadai ta samu yana ta rubuce rubucensa a wani katon littafi,ko da yaji shigowar mutum sai ya daga kansa domin ganin waye.Oh my God, ya fada cikin harshen turanci.lokacin da yaga Bookie ce tsaye a bakin kofar babu alamun faraa a tare da ita. Hi Dr dowsontace da shi lokacin datake kokarin karasowa inda yake zaune.cikin bacin rai Dr Dowson yamike tsaye tare da kallon Bookie,Nace dake bazanyi abinda kike son aikatani dole ba,shin wai ke bakyason rayuwarki ne,meyake damunki ne,kuma meyesa kike son aikata hakan ne akanki? duk yayi wannan tambayar ne cikin harshen turanci kasancewarsa farar fata ne,kuma kwararran likita maiji da kansa akasar AMERICA. Good question Bookie tace dashi tana kallonsa,wannan lokacin hartafi taimasa. Zauna to zanyi ma bayanin dalilin da yasa na nace dole sai kayimini abunda nake so Bookie taci gaba bayan Dr Dowson yazauna kan kujerar tasa. Nayarda da kaine shiyasa har nazo maka da wadannan bukatar tawa Dr Dowson,nasan kuma zaka iya biyamun wannan bukatar tawa, kodan amincin dake tsakanin muBookie taci gaba. Kamar yadda nasanar dakai abaya shine kawai inasone kayimin allura wacce zata daukeni tsawon kwana arbain kafin tafara aiki akaina,kuma ba allurar mutuwa zakayimin ba illa wacce kawai zata gusar min da hankali na ne har tsawon kwana daya tak. Dallin da yasa nacema haka shine,ina so zandauki fansa ne akan masoyina jakson dan cin amanar da yayi mini. Dr dowson yai shiru kawai yana saurarta da kuma binta da idanuwa kawai. Na hadu da Jackson ne wata guda da yawuce a wani club na gidan rawa a inda kuma ya nuna yana sona,banyi wata wata ba nima na yarda dashi muka fara soyayya,sai daga bayane nagane ashe Jackson yana yin soyayya da wata bayanni,shine abin yai matukar batan rai shine nake son naga na hallakasa kawai domin huce takaici na da rama abinda yaimin. wannan lokacin sai da Dr Dowson yamike tsaye dayaji abin har yakai dayin kisan kai. Duk wannan maganganun da sukeyi sunayi ne da turancin america. Kina hauka ne Bookie,? Kisa fa kikace? Kwarai kuwa kisa ta amsa masa da gaggawa. Kaga Dr Dowson duk wannan abin banatashin hankali bane kana jina ko?Bookie tace dashi.sannan kuma taci gaba. Idan har kayimin allurar nan to natabbata zata taimaka mini matuka. Ta ina zatatai maka miki,nidai banga ta inda allurar zatayi aiki a nan ba. Dowson yafada a dan tsorace. Murmushi kawai tayi sannan ta dora daga inda ta tsaya. Idan nayi kisan to natabbata yan sanda zasu kamani,daga nan kuma bazasuyi wata wata ba zasu mikani ga court ne dan zartar mini da hukuncin da yadace akaina ne.Bayan ankaini prison kuma to anan allurar zatayi aikinta. Kaga idan akaga nafadi babu rai to za a dawo dani ne domin yimin janaiza,bayan an rufeni sai kai kuma kaje katone kabarin nawa kafuto dani,daga nan kuma ni zandora daga inda natsaya ne. Dr Dowson yai shiru kawai yana sauraronta har ta karasa bayanin nata. Murmushi yayi kawai da yafiskanci inda Bookie tasa gaba. lallai baki da dama bookie yace da ita.daga bisani yadora daga inda yatsaya. Nawa ne ladan aikin nawa,domin dai kinsan wannan aikin kasadarsa tafi ribarsa yawa,kuma nikaina zandandana kudata da zarar asirinki yatonu. Bookie tayi dariya karonta na farko,sannan tace.Bana bukatar kadamu a cikin wannan planning din nawa,nice nake da tsarin komai,akwai hanyoyi da dama da zan kubutar dakai. wai shin kai har kana tunanin cewa balli zaitashi ne? Bookie tayi masa tambaya. Kedai bari kawai ai ba acewa koma,domin dai kinsan bincike bakarya bane ya fadi hakan yana zuba mata idanuwa kawai yana kallonta. zanbaka 50 million dollars. Bookie tace dashi tana kallonsa. Cikin rawar jiki yamike tsaye,kai tsaye wajan da yake aje allurorinsa ya nufa cikin zumudi. Kada kidamu Bookie anyi angama kawai yace yana murmushi tare da tunanin kudin da Booki zata bashi. Mr~jameel
Posted on: Sat, 30 Aug 2014 11:30:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015