MARABA da RAMADAN* (17) Wata rana MANZON ALLAH S.A.W Yazo zai hau - TopicsExpress



          

MARABA da RAMADAN* (17) Wata rana MANZON ALLAH S.A.W Yazo zai hau kan minbarinsa mai hawa 3 yana taka hawan farko sai yace AMIN ya taka na biyu yace AMIN ya taka na uku yace AMIN*** To bayan da ya gama ya sauko, sai SAHABBAI suka tambaye shi, ya “rasulullahi“ dazu da zaka hau munbari munji kana cewa AMIN har sau 3 mi ya faru*** Sai ANNABI MUHAMMAD S.A.W yace mala,ika jibrilu ne yazo yana addu‘a ni kuma ina cewa AMIN sahabbai suka ce wace addu‘a ya kawo mana*** Manzon Allah yace, jibrilu yace 1-Duk wanda ya riski iyayensa 2 ko 1 da ransu, amma bai kyautata musu ba, to ALLAH ya nisanta shi daga RAHMA, ya nisanta shi daga cetonka, ANNABI yace AMIN*** 2-Duk wanda AZUMI yazo har ya wuce bai nemi gafarar ubagiji ba, daga laifukan daya aikata, to ALLAH ya nisanta shi daga RAHMA ya nisanta shi daga cetonka, ANNABI yace AMIN*** 3-Duk mutunin da akace (ANNABI-MUHAMMAD) yana ji amma baice....sallallahu alaihi wassalam ba....ko yayi masa SALATI* to ALLAH ya nisanta shi daga RAHMA ya nisanta shi daga cetonka, ANNABI yace AMIN*** HADISI ne ingantacce, ALLAH ya kubutar damu daga HALLAKA.......!!!
Posted on: Thu, 25 Jul 2013 20:15:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015