ME YA FARU A KARBALA 17 Husaini Ya Kama Hanyar Kufa Safiyar 8 ga - TopicsExpress



          

ME YA FARU A KARBALA 17 Husaini Ya Kama Hanyar Kufa Safiyar 8 ga watan dhul hajji a shekara ta 61H ita ce ranar Tarwiya; ranar da alhazai suka kama hanyar zuwa Minna don fara aikin hajji. Ita ce kuma ranar da kaddarar Allah ta fitar da sayyidina Husaini daga garin tare da iyalansa zuwa ga darajar da madaukakin sarki ya ajiye masu ta samun shahada a Karbala. Al-Bidayah Wan Nihaya na Ibnu Kathir (8/171). Abdullahi dan Umar (R.A) wanda a da suka dauki matsayi iri daya da Husaini (R.A) kafin nadin Yazid a yanzu sai da ya bi abokinsa Husaini har tsawon tafiyar kwana biyu yana kokarin shawo kansa, yana ce ma sa ka tuna rashin kirkin mutanen Iraqi da rashin cika alkawarinsu. Wace irin wahala ce mahaifinka bai sha a hannunsu ba? Kuma wace irin tozartawar ce ba su yi ma yayanka Al-Hasan ba?. Daga karshe Husaini ya dauko tulin takardunsu ya nuna ma sa. Da Ibnu Umar ya hakikance ba zai iya shawo kansa ba sai ya rungume shi yana bankwana da shi kuma ya fadi wata kalma mai ban tausayi wadda ke nuna ya hakikance Husaini ba zai kai labari ba. Yana mai zubar da hawaye ya ce ma sa: أستودعك الله من قتيل! Ina ba da ajiyarka ga Allah ya kai wanda wanda za a kashe!. Martanin da sayyadi Husaini yake maida ma duk masu bashi shawara shi ne Allah ya saka maka da alheri. Na fahimci duk abinda kake nufi na shawara da nasiha. Ina gode maka a kan haka. Abinda Allah ya nufa kuwa shi zai faru ko na yi aiki da shawararka ko ban yi ba. Idan mutum ya kwatanta matsayin Husaini da na dan uwansa Al-Hasan dole ne ya sha mamaki. Al-Hasan dai nadadden sarki ne da yan Shiar mahaifinsa suka taru suka nada shi bayan cikawar mahaifin nasa. Akalla yana tare da runduna mai yawan sojoji sun kai 100,000. In da ya so sai ayi shekaru ana yaki da Muawiya da jamaarsa. Amma sai ya fifita zaman lafiya a kan zubar da jinainan musulmi. Don haka ya nemi Muawiya da kansa suka sasanta, ya dauki ragamar alumma ya rataya ma sa, ya kuma sa duk jamaarsa suka yi ma sa mubayaa. Da haka sai alumma ta samu kwanciyar hankali akalla na tsawon shekaru 20 da Muawiya ya yi a kan karagar sarauta. Amma shi Husaini saboda hukuncin Allah bai kalli irin abinda wansa ya kalla ba da aka zo wannan lokaci. Domin ya fito zuwa Kufa ba shi tare da kowa sai iyalansa. Wadanda kuma ya dogara ga gudunmawarsu ba masu fidda kitse wuta ne ba. Mutane ne da aka san su da munafurci da yaudara. Ga su kuma da tsoro da kwadayin abin duniya. A cikin hudubobin sayyadi Ali (R.A) da ke cikin Nahjul Balaga ya sha fitowa fili ya zarge su da haka. Haka ma a littafan Shia da dama an zargi mutandn Kufa da haka. Duba alal misali Mausuat Ashura na Jawad al-Muhaddithi da kuma Fi Rihabi Ashura na Husain al-Kourani. A wurin Ahlus Sunna Hasan da Husain (shugabannin matasan aljanna) sun yi ijtihadi ne. Kuma la budda dayansu ya yi daidai, daya kuma ya yi kuskure. Amma yan Shia sun ce dukan su maasumai ne da ba su tuntube. To, ko me zasu ce a kan wannan? Via Dr Mansur Sokoto
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 08:14:34 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015