MU SHA DARIYA. JARABAWAR ALJANI! Wasu mutum uku ne suke - TopicsExpress



          

MU SHA DARIYA. JARABAWAR ALJANI! Wasu mutum uku ne suke tafiya a jirgin ruwa, da Baturen Amurka da na Jamus da kuma dan Najeriya. Kwatsam sai ga aljani ya bayyana ajirgin kuma ya ce zai kashe su idan ba su cika ka’idojin da zai shimfida musu ba. Aljani ya ce: “Idan kowane daga cikinku yana son ya tsira da ransa to tilas ne ya jefa wani abu a cikin kogi kuma ya kasance abin da za ku jefa wanda ni ba zan iya daukowa ko gani ba ne.” Nan take Baturen Amurka ya mamaye shi ya jefa makallin rigarsa a cikin kogi. Aljani ya bi shi kuma ya ciro, sai ya kashe shi. Shi kuma Baturen Jamus sai ya jefa allura cikin ruwa, nan ma aljani ya bi ya dauko kuma ya kashe shi. Da aka zo kan dan Najeriya sai ya kalle ledar ruwan fiyawota da ke hannunsa, ya zuba ruwan cikin kogin ba tare da ledar ba, ya ce wa aljani: “To ina so ka debo mani daidai ruwan da na zuba a kogin in da gaske kake.” Nan fa idon aljani ya raina fata kuma dan Najeriya ya tsira.
Posted on: Fri, 08 Nov 2013 06:59:52 +0000

Trending Topics



been on google reading senzo

Recently Viewed Topics




© 2015