Mace-Tagari .........CI GABA DA BAYANIN NAUIKAN JINI GA - TopicsExpress



          

Mace-Tagari .........CI GABA DA BAYANIN NAUIKAN JINI GA YA MACE:- Bayan Jinin Alada wanda bayaninsa ya gabata akwai kuma jinin Haihuwa wanda mace ke fara zubar da shi yayin da take daf da haihuwa ga bayaninsa kamar haka: 2. Jinin Haihuwa: Jini ne da ya ke fitowa mace yayin da haihuwa ta gabato kuma yakan ci gaba da fita har bayan haihuwa, wasu matan sati 2, wasu kasa da kuma sama da haka, amma galibi yakan dauki kwanaki kafin ya tsaya amma Malamai sun iyakance tsayin kwanakinsa da kwana (50) duk macen da ta kai tsawon kana hamsin bai tsaya ba a wannan lokaci za ta yi wanka ta kuma ci gaba da sallah da duk ibadu baki daya. Ya kan riga zuba ne tare da gudaddadi wani lokaci tsinkakke wani lokacin kuma mai kauri, sannan ya yin da ya zo karshen shima wani ruwa mai wari kamar na jemammiyar fata yana zuba a karshensa, galibi mata sukan sanya auduga tsawon wuni guda don tabbatar da daukewar wannan jini, kuma shi wannan ruwa yakan dauki lokaci yana fita don wani lokaci bayan mace ta yi wankan tsarki ma yakan fita don haka kar ta dauka cewa har yanzu batayi tsarki ba za ta ji gaba da sallah sai fa in jini ne ya dawo to a wannan lokaci zata bar yin sallah har sai ya dauke kuma ta ci gaba da lissafa kwanakinta. 3. Jinin Cuta: Malamai sun yi bayani akan wannan masala amma a takaice shi ne; ya yin da mace jinin aladarta ya wuce adadin kwanakinsa za ta kara har zuwa kana 15, ko kuma jinin yakan zo mata ya dauke kana daya ko biyu to zata tara adadin kwanakin jinin har sukai 15, duk lokacin da kwanaki suka cika kuma ta tabbatar kalar jinin ya canza da yadda ta sanshi sai ta yi wanka ta ci gaba da sallah da sauran ibadu. Daga nan sai ta nemi magani. Amma idan har tazatar jinin ya kai kwanaki 10 ko fiye a cikin wata to wasu malamai suna ganin aladace mai zaman kanta maana tayi alada biyu kenan a wata daya, wasu kuma suna ganin ci-gaba ne da waccan aladar tata musamman idan hakan shine dabiarta jini daya a wata. Abu mai muhimmanci shine mace ta kiyaye kalar jininta da kuma adadin kwanakinsa. Amma akan sami canjin adadin kwanakin jinin alada ga mace musamman wacce ta yi haihuwar fari wani lokaci jinin yakan canza salo. Haka kuma ga mata masu shan magunguna da suke da alaka da mahaifa ko allurai don hana daukar ciki suma jininsu yakan rikice wani lokacin yakan cakude ta kasa banbance na alada da na cuta don haka dai mace mai nutsuwa da kaifin basira itace zata taimaka miki wajan banbance jininki kuma aje ga likitoci don tabbatarwa. Haka ma mai jego ya yin da adadin kwanakin da muka ambata suka cika amma jini bai tsaya ba, a wannan lokaci za tayi wanka ta ci gaba da ibada sai kuma ta nemi magani. Hukuncin wannan jini aduk lokacin da ya fito shine tsaftace jiki da tufafi amma ba wanka ba, idan kuma mace tayi (kunzugu) to sai ta riga sake alwala a kowacce sallah. Allah shi ne mafi sani, in sha Allahu Siffar wanka tsarki shima zamu yi bayaninsa nan ba da jimawaba kamar yadda mu ka alkawarta. Ya Allah ka samu cikin mutanen da suke da tsarkin zuciya da na jiki ameen.
Posted on: Wed, 20 Nov 2013 08:55:23 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015