*****Mu Sha Dariya***** Wani Alhaji ne yake yawan takurawa - TopicsExpress



          

*****Mu Sha Dariya***** Wani Alhaji ne yake yawan takurawa direbansa, shikuma direban yanason ya rama irin wulakancin da Alhajin yake yimasa. Watarana Alhaji ya fadawa direban nasa zasuyi tafiya zuwa wani gari. Da gari ya waye sai suka dauki hanyar wannan tafiya tas, suna cikin tafiya sai Alhajin yace da direba ya tsaya, saboda yanajin fitsari zayyi, nan take sai direba ya tsaya, Alhaji ya fita fitsari, yana cikin yin fitsarin nasa, sai direban ya sauka a mota yazo a guje da kafa ta gaban Alhajin yanata gudu. Shikuma Alhjin kawai ba tare da tambaya ba, shima sai ya jona masa da gudu. Suka dinga gudu, har sai da sukaje nesa, har Alhajin yagaji da gudu harma Yana Fuka (Nishi):- hyn hyn Hyn Yace:- direba me ya faru kake ta gudu? Sai direban Yace: Alhaji motsa jiki nake (excercise) ne kawai nakeyi. Source: #Maryam Maifada Editor: #Anwar
Posted on: Tue, 03 Sep 2013 08:17:37 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015