NI FA SHASHASHA NE Wata rana Shehu Jaha ya tafi ya kai alkamarsa - TopicsExpress



          

NI FA SHASHASHA NE Wata rana Shehu Jaha ya tafi ya kai alkamarsa wajen nika, da ya isa gurin sai ya rika diban tafi daidai daga buhunan mutane yana zubawa a buhunsa. Sai mai nika ya ce: Lafiya kuwa, menene haka? Sai ya ce kai ni fa shashasha ne, duk abinda hankali na ya shirya mini shi nake yi. Sai mai nika ya ce: To, idan kai shashashane me yasa baka debo alkama daga buhunka ka zuba a buhunan mutaneba? Sai ya ce: Ai ni shashancina mai sauki ne, idan kuwa na aikata abin da ka fada, sai na zama shashasha hawa biyu.
Posted on: Tue, 06 Aug 2013 21:25:43 +0000

Trending Topics



>
Clearance Deals on Panasonic PT60LC14 Lamp with Housing TY-LA1000

Recently Viewed Topics




© 2015