RANAR MALALA A DUNIYA MALALA A NIJERIYA Kusan zamu iya cewa - TopicsExpress



          

RANAR MALALA A DUNIYA MALALA A NIJERIYA Kusan zamu iya cewa itace yarinyar datayi fice a cikin shekaru uku a mashahuran duniya, itace kuma wacce tasamu tagomashin turawa da majalisar dinkin duniya, musamman akan yakin datakeyi da fafutukar ganin mata sun sami ilimi mai nagarta domin suma adama dasu a duniya, kuma. Itace yarinya daya tilo da majalisar dinkin duniya ta ware ranar ranar 12 ga watan juli don tunawa da irin fafutukar datakeyi, awannan shekara Malala Yousafzai tayi bikin cikar shekararta goma sha bakwai a kasar nijeriya inda ta tattauna da shugaban kasar kan bawa mata ilimi dakuma maganar yaran da aka sace a chibok, takuma tattauna da yan kungiyar nan na asako yayanmu, kafin nan tukunna wacece MALALA YOUSAFZAI ? An haifi Malala agarin pakistan a garin Mingora ranar 12 ga watan julayi, takuma halacci wata makaranta Khusal public school, tun ayarintar ta tafi son fannin karatun likitanci, amma mahaifinta ziauddin ya karsasheta akan ta karanci tsarin shugabanci da siyasa, mahaifinta ya bayyana amatsayin wata yarinya mai hazaqa da baiwa, inda yabata dama data tattauna batutuwan siyasa koda acikin dare ayayin da kannenta biyu sukayi bacci. Malala tafara magana ne a cikin alumma a karshen watan satumbar 2008, lokacin da yan taliban suka hana yan mata halartar makarantun Boko, inda agurin taron da aka hada a peshawar ta gabatar da lakca me jan hankali, ta yaya yan taliban zasu danne haqqin zuwa makaranta danake dashi ? Wannan itace tambayar datayi alokacin taron da ake dauka agaban yan jaridun gidajen redio da talabishin dakuma mujallu. Wannan qasidar data gabatar da dauki hankalin mahukunta kasar pakistan da apganistan, inda har sai da shugaban yan taliban Maulana Fazlullah ya sanya aka rufe gidajen talabijin da rediyon da suka yada wannan maqalar, wanda alokacin tana cikin shekaru na 11 ne, awannan lokaci kowa na tsoron kungiyar yan taliban, sun hana mata zuwa makarantu, zuwa siyayya manyan kantina (supermarket), inda ranar 3 ga janairun 2009 Malala tasaki wani rubutu a yanar gizonta inda tace daga cikin dali6an ajinsu 27 mutane 11 ne suka halacci makaranta aranar saboda tsoron yan taliban, a Mingora yan taliban suka futar da wata sanarwar hana mata zuwa makaranta daga ranar 15 ga janairu, yan taliban sunci gaba da rushe makarantu, yayinda ita kuma Malala taci gaba da jajircewa wajen nunawa mata yan uwanta mahimmancin karatu, tareda kiran su da su dena amfani da tsoratarwar yan taliban sufito su tafi makaranta domin sunada yancin hakan, adede wannan lokacin ne takuma yin wani rubutu inda ta danganta yan taliban da masu kashe ilimin mata inda ayanzu mata 70 ne ke halartar makarantu a cikin dali6ai sama da 700, wanda a cikin kwanakin nan ne akaji harbin bindiga a garin Mingora kauyen da Malala take zaune, amma mahaifinta yaci gaba da bata kwarin gwuiwar akan kar taji tsoro taji gaba da gwagwarmayar datakeyi wajen nunawa mata mahimmancin karatu, aranar 18 ga fabrairune shugaban yan taliban yayi sanarwar mata zasu ci gaba da halarta makarantunsu har lokacin da zaayi jarrabawa a watan Mayu, tun daga wannan lokaci farinjinta yaci gaba da daukaka, mutane sukaci gaba da karanta qasidunta a shafin yanar gizonta, gata yarinya karama amma yan jaridu sunci gaba dakai mata farmakin suyi hira da ita, to amma sai mahaifinta ya kar6i wata barazanar kisa daga yan taliban, amma duk da haka Malala taci gaba da jajircewa wajen hada lakcoci da yan uwanta mata tareda basu bayanai masu mahimmanci akan yanda zasu nemi ilimi, daga nan ne kuma tafara samun kyaututtuka daga kungiyoyi harma da gwamnatin kasar pakistan, inda firaministan kasar Yousaf Raza Gilani yabata kyautar Zaman lafiya ta kasar, A ranar tara ga octoban 2012 ne Malala ta fuskanci kanta awani hatsari na neman halakata bayan ta dawo daga makaranta, inda dan bindigar a cikin 6oyayyar fuskarsa da bakin kyalle ya rutsata ita da sauran yan uwanta yan makaranta yana tambayarsu wacece Malala ? Idan kuma basu fada ba duk zai harbesu da bindiga, kafin suyi wata magana sai taji saukar harsashi akanta, yakuma gogi kafadarta.....cikin gaggawa aka kaita wani asibitin sojoji domin aceto ranta, wanda aka cire harsashin bayan shafe awa uku ana mata aiki wanda saura kadan harsashin yayiwa lakarta illa, amma kuma bata cikin hayyacinta sannan kuma akwai alamun kota tashi zata iya naqasa, wannan yabada damar futa da ita kasar jamus don nema mata lafiya, inda gwamnatin kasar da dauki nauyin biyan duk abinda zaa kashe, bayan shafe wasu yan kwanaki sai aka dauketa aka maida ita kasar ingila domin karaci gaba da bata kulawa dakuma lafiyarta, aranar 17 ga watane tafara dawowa hayyacinta inda daktocin kasar sukace saura kadan kwakwalwarta tasamu matsala, aranar 20 ga watane kuma harta fara yin rubutu a shafinta dauke da hotonta akan gado a asibin Sarauniyar Ingila dake garin Birmingham, bayan sallamarta daga asibitin, aka koma da ita wani guri da ake kira midlands inda aka kuma yi mata tiyata don kara daidaita kashin bayanta dakuma maganarta, wannan harin ne kuma ya janyo zanga-zanga tasama da mutane miliyan 2 akasar pakistan masu goyon bayanta dauke da kwalaye an rubuta yancin karatu mukeso inda kasar tasanya rupee miliyan dubu 2 ga duk wanda yagano maharan, yayinda shugabannin duniya sukaci gaba da Allah wadai da wannan harin, Shugaban majalisar dinkin duniya Banki-Moon, dakuma Shugaban kasar Amurka, da Hillary Clinton, mawaqiyar amurka Madonna ta sadaukar da waqarta ta Human Nature ga Malala, Angelina Jolie da matar tsohon Shugaban Amurka Laura Bush, duk sun yi Allah wadai da harin, Shugaba Amurka Obama da tsohon firaministan Ingila Gordon Brown duk sun dubata a asibiti. Bayan kwanaki kadan ne gwamnatin kasar tace takama wanda ya harbeta, matashi Atta Ulah Khan dan taliban shine wanda yayi harin, Malala taci gabada yaqi da nemawa mata yanci a guraren maqalu, da kasashe harma da gwamnatocin kasashe, ita mace mafi yarinta datake da alaqa da manyan kasashen duniya, kuma ta lashe kyautar nan ta majalisar dinkin duniya Noble Peace Prize, tun daga wannan lokaci majalisar dinkin duniya ta futar da ranar sha biyu ga wata domin tunawa da wannan yarinya, wacce ta gabatar da Maqala agaban Majalisar dinkin Duniya akan Ilimin yaya Mata........ Zuwanta nijeriya nada nasaba da yaran da aka dauke yan makarantar chibok, kuma ta gargadi Shugaba Goodluck da abi duk wasu hanyoyin kwarai domin kwato wadannan yara, wadannan yara yan uwanane, kuma kawaye nane, kullum suna zuciyata, bana iya bacci, wannan dalili ya sanya nazo na jimamawa iyayensu, kuma naga sauran da suka gudu, zuciyata cike take da quna da firgici akan halin da yan uwana suke ciki, addininmu na Musuluncci yayi hani da fasa kwaurin mata...ina sonku, zanci gaba dayi muku addua dare da rana wannan kalamin Malala ne lokacin datake ganawa da kubutattun matan chibok, sannan kuma tace ta sadaukar da wannan rana ta murnar haihuwarta ga wadannan yan mata, takuma jinjinawa yan kungiyar BringBackOurGirls sannan ta kuma kara karfafa mahimmancin ilimin yara mata....... Dafatan wannan ziyara ta wannan yar gwagwarmaya zata amfanemu.. Sunusi Mailafiya 14-07-2014
Posted on: Mon, 14 Jul 2014 19:13:04 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015