RIKICIN PDP: Gwamnati Na Gallazawa Yan Sabuwar PDP Akwai - TopicsExpress



          

RIKICIN PDP: Gwamnati Na Gallazawa Yan Sabuwar PDP Akwai kwararan zaton dake nuni da cewa Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gallazawa yayan sabuwar PDP, domin nuna musu kuskuren su na neman ruguza jamiyyar PDP, ta hanyar ballewa daga jamiyyar suka kafa bangaren su daban. A baya - bayan nan bayan hukumar birnin tarayya ta rufe masaukin gwamnan jihar Adamawa dake Abuja, haka hukumar ta aika wa Sanata Aisha Al-Hassan takardar rushe wani katafaren wurin taronta mai suna A-Park da yake kusa da OAU, a yankin Maitama, Abuja. Binciken #RARIYA ya nakalto cewa tuni Hajiya Aisha, wadda sanata ce daga jihar Taraba, ta tattara takardunta don kalubalentar wannan mataki, saboda a cewarta kafin ta gina wurin taron sai da ta samu sheda daga hukumar tsara gine - gine ta birnin tarayyar. Shi ma tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje ya gami da fushin gwamnatin inda aka dakatar jamian tsaron dake kula da lafiyarsa kamar yadda aka yi wa tsohon gwamnan Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, wanda dukkan su ke cikin sabuwar PDP ta su Kawu Baraje. Shugaban sabuwar PDP da sakatarensa na jihar Bayelsa, su ma yan sanda sun bayyana su a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo. Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso shi ma gwamnatin ba ta bar shi ba, ta kwace takardar shedar wani gida mallakinsa, sannan a baya an rushe shugabannin jamiyyar PDP reshen jihar ta Kano, an kuma maye kurbin su da shugabannin rikon kwarya. A martanin da sabuwar PDP ta yi game da faruwar wadannan abubuwa, sakataren jamiyyar Chief Eze Chukwuemeka Eze, ya bayyana hakan a matsayin koma baya a bangaren demokradiyyar kasar nan da har yanzu take a matakin rarrafe.
Posted on: Wed, 16 Oct 2013 07:25:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015