SOJOJIN Kasar Burkina Faso sun nada tsohon ministan harkokin wajen - TopicsExpress



          

SOJOJIN Kasar Burkina Faso sun nada tsohon ministan harkokin wajen kasar Michel Kafando a matsayin shugaban kaas na rikon kwarya a wani yunkuri na mayar da kasar turbar demokradiya. Nada Michel Kafando ya biyo bayan dogon tattaunawa tsakanin sojoji, yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula sakamakon bukatar kungiyar kasashen Afrika na ganin an mayar da kasar turbar demokradiya cikin makwanni biyu. Kafando mai shekaru 72, tsohon Jakadan Burkina Faso ne a Majalisar Dinkin Duniya, kuma ya taba shugabancin kwamitin Sulhu, a karkashin shugabancin Blaise Compaore. Ana saran Kafando ya nada Fira Ministan da zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar da zata kun shi ministoci 25, sai dai yarjejeniyar ta nuna cewar ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba. Sabon shugaban ya bayyana nadin nasa a matsayin wani karimci da aka masa, inda yake cewar zai yi iya bakin kokarin sa dan aiwatar da shi.
Posted on: Mon, 17 Nov 2014 04:29:39 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015