Sauran kwanaki 34 ayi zaben Shugaban kasa a NijEriya, Yanuwana - TopicsExpress



          

Sauran kwanaki 34 ayi zaben Shugaban kasa a NijEriya, Yanuwana Yan Nijeriya masu hankali da tunani, idan zamuyi zabennan muyishi da sunan Allah, sannan mu dubi wadannan abubuwa kamAr haka: Masallacin Sarkin Kano Maluman addini daaka kashe mana Sarakunanmu daaka kashe mana Yanmatan Chibok Daliban Buni Yadi Daliban Potiskum Satan kudin man petur Satan kudin pension police Satan kudi 20billion $ million 9 na sayan makamai Luguden boma-bomai daake mana Daukar maaikatan immigration Farashin litren man petur Faduwar darajan naira Satan albarkatun kasa Rashin wutan lantarki Sayar da NEPA Sayarda matatun albarkatun kasa Trippling na kudin wuta Yajin aikin jamioi Yajin aikin health wokers Korar sojoji a aiki Daurewa yan taadda gindi Daurewa wassu tsirarun mata irin su Stella oduah da Alinson Madueke gindin zama Yadda aka wulakanta yan majalisu (dukdama suma sai a slow) Mutuna cewa sojojin sunce a basu makami domin yaki da boko haaram sai kawai aka basu hukuncin kisa maimakon makamai Mutuna yadda yanuwanmu ke watse a refugee camp, mutuna yadda sanyi da yunwa take kashesu, mutuna yadda wassu garuruwan suka zamo tarihi, mu tuna yadda suka creating mana artificial talauci, mu tuna yadda suka creating BH dun su wargaza mana kasarmu. Mu kuma tuna cewa Yan PDPn: Basu tara 21billion domin kawar da Ebola ba Basu tara 21 billion domin gyaran asibitoci ba Basu tara 21 billion domin sayan magani ba Basu tara 21 billion domin sayawa sojojinmu makamai na fada da Boko Haraam ba Basu tara 21 billion don taimakawa wadanda fari ya aukawa ba Basu tara 21 billion domin rigakafi wa kananan yara ba Basu tara 21 billion domin mutanen daaka konewa gidaje, masallatai da shagunaba, amman dukda hakan sun tara 21 billion domin aci gaba da mayar da garuruwa kufayi, kananan yara marayu, matan auren zaurawa, mutane mabarata kamar yadda wannan azzalumar gwamnatin tayitayi tun daga hawanta karagan mulki har yau. Hausawa sukace: Jiki Magayi. Kowa yasan mun suburbudu a wajen wannan gwamnati masu Ebele da Ebola, Shekkau da Shekarau. Ya Allah Ka agajemu, Ka tallafa mana, Ka tausaya mana domin Kaine Kafi kowa tausayi, Kaine Mai juya alamura Ya Arhamar Raheemina mun tuba ba don halinmuba Ya Allah Ka canja mana wannan gwamnatin zalunci, Ka daura mana shugabanni nagari masu tsoron azabarKa da kuma kaunar Rahamarka.
Posted on: Sun, 11 Jan 2015 05:24:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015