Shehu Ibrahim Niasse RTA Yana Cewa ***** Inai muku wasiyya ku kula - TopicsExpress



          

Shehu Ibrahim Niasse RTA Yana Cewa ***** Inai muku wasiyya ku kula da sirrin ku,koda kuwa sirrin daya shafi duniya ne,domin. Duk wanda ya boye sirrinsa haqiqa ya Mallaki rayuwar sa da komai nasa Ku lazimtawa kanku haquri abisa dukkan wata jarrabawa da Allah zai muku,ku tabbata cikin masu yarda da duk wata Qaddara Kuso juna dan Allah,ku ziyarci junanku dan Allah,ku zauna da junan ku dan Allah,ku lazimtawa kanku hidimar shehunnanku,sufaye suna cewa Wanda duk ya hidimta mana zamu gabatar dashi cikin halarar Allah ba tare da himmar sa ce takai shi ba Kada ku yanke zumuncin yan uwantaka ta Allah da take tsakninku,kada kuma ku juya wanin ku baya a bisa wani kuskure daya aikata,kada kuyiwa junan ku hassada,kada kuqi junanku dan san zuciya,ku zamo Bayin Allah yan Uwan juna cikin Allah
Posted on: Mon, 09 Sep 2013 06:25:12 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015