So yasa na taɓu-ta-kai inji AZIMAT KEFFI. Sunana azimat, yar - TopicsExpress



          

So yasa na taɓu-ta-kai inji AZIMAT KEFFI. Sunana azimat, yar shekaru ashirin da biyu, mahaifina haifaffen keffi ne, yana ɗaya daga cikin masu sarauta a keffi, sannan jigo ne a gwabnatin tarayya. Mahaifiya ta yar yola ce, yanzu muna zaune a birnin tarayya, tunda nake sau ɗaya na taɓa zuwa garin mama na, dan haka duk wasu danginta ban sansu ba. Wata rana mukayi baƙon wani saurayi, daga yola, tun kafin yazo naji labarin zaizo, zai zauna a gidan mu, zai ringa zuwa jamia. Tunda naganshi, naji zuciyata ta buga tashin farko, ban san ko waye ba, nasan de sunansa musab musa, da daddare ban iya runtsawa ba, kawai ina tunaninsa, ina tunano surarsa. Tun daga lokacin sonsa ya kamani, koyaushe ina maƙale dashi, yana bani labarai kala-kala, idan ya tafi makaranta, har addua nake ya dawo da wuri, mu zauna tare, idan zai ɗan zaga gari tare muke tafiya a motata, na shaƙu da shi ainun, na zama ina bin raayinsa, duk abinda yake so, shi nake so nima, har so nake nayi abinda zai birge shi, yayi farin ciki, ada bana shiga cikin, amma idan yace yana shaawar wani abu, gudu-gudu sauri-sauri nake dafa masa. Abin ya zamar min balai tsakar dare sai na farka na kama tunaninsa, sai naga kamar gari bazai waye da wuri ba, idan nayi bacci kuwa, mafarkinsa nake, bani da magana da zance sai nasa, jarabar-sonsa ya kamani tamau. Wani lokaci mukai kwana biyu bamu haɗu, na shiga damuwa sosai, bashi da free tym saboda sun kusa fara jarabawa, a wannan lokaci ne damu, har takai kowa ya gane damuwa ta, mahaifiyata tai kirana ɗakinta, tace meye yake damunki ne nace mata ba komai, ta dubeni, sannan tace ke bari kiji na faɗa miki, ba tun yanzu ba nasan inda kika dosa, abinda kike tunani ma bazai yuwu ba, musab da kike gani kawunki ne, ƙane nane, uwa-ɗaya-uba-ɗaya, kuma ma yana da wadda zai aura a ƙauye. waɗannan sune munanan kalamai dana taɓa ji a rayuwa ta, ku taya ni da addua allah ya yaye min JARABAR-SON kawuna. Gaskiya duk mai irin wannan soyyayya namiji ko mace, abin a tausawa ne, jarabar so ba daɗi. Jamilu zainab.
Posted on: Tue, 19 Nov 2013 20:52:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015