TATTUNAWA TSAKANIN UMMUL MUMININA A’ISHA DA UMMUL MUMININA UMMU - TopicsExpress



          

TATTUNAWA TSAKANIN UMMUL MUMININA A’ISHA DA UMMUL MUMININA UMMU SALAM (RA) Malaman tarihi sun ruwaito cewa lokacin da Ummul Mumina A’isha ta yanke shawaran shiga cikin rundunan da zasu je su yaki Imam Ali (AS), Ummu Salma ta sameta take ce mata: “Kin tuna wata rana muna tafiya tare da Manzon Allah (S) sai ya wuce mu yayi gefen hagu da (wurin da ake ce ma) Kadid, ya zauna tare da Ali, suka jima suna tattaunawa, kika ce min sai kinje kin same su, nayi ta kokarin hanaki amma kika ki magana na kika je (wurin su). Baki jima ba sai gashi kin dawo kina kuka, na tambayeki: ‘Me ya faru?’, sai kika ce min: ‘Na same su ne suna tsakiyan tattaunawa sai nace wa Ali: ‘Ina da kwana deya ne kawai cikin kwanaki tara tare da Manzon Allah (S), to baza ka barni (da shi ba) ya kai dan Abu Dalib! Ka barni da shi mana a rana na’, sai Manzon Allah (S) ya juyo alhali yana cikin fushi sosai yace min: ‘Ki koma! Wallahi ba mai kinsa sai marar imani’. Sai kika juyo cikin nadama da bakin ciki”, sai A’isha tace “E, na tuna shi”. Sannan sai Ummu Salma ta sake ce mata: “Yanzu baki tuna cewa wata rana ni da ke mun kasance tare da Manzon Allah (S) sai yace mana: ‘Waccece a cikin ku za tayi tafiya a akan rakumi har karnukan Hau’ab suyi mata haushi, kuma ta bar han`yan gaskiya?’, sai muka ce: ‘Muna neman tsarin Allah da manzonSa a kan wannan’. Sai ya taba bayanki yace: ‘Kada ki kasance wannar Ya Humaira!”. Aisha tace: ‘Na tuna shi”. Ummu Salma ta kara ce mata: “Kin tuna ranan da mahaifinki suka zo shi da Umar, sai muka san`ya hijabanmu, sannan suka shigo ciki, (suka samu Manzon Allah (S)) sukayi duk maganan da ya kawo su har suka ce: ‘Ya ma’aikin Allah! Ba mu san yaya zaka jima tare damu (a duniya) ba, kuma kaine kadai zaka iya fada mana waye zai khalifance ka a kan mu, ta yadda bayanka zamu san gun wa zamu je’. Sai Manzon Allah (S) yace musu: ‘Ni naga matsayin sa (a wurin ku), in da zan`yi haka to da duk zaku rarrabu (ku juya baya) kamar yadda bani Isra’ila suka juya wa Haruna baya’. Sai sukayi shiru (na wani lokaci) sannan suka tashi suka fita. Bayan sun tafi sai muka kariso gun Annabi (S) alhali ke ce a gaba, sai kika ce masa: ‘Ya ma’aikin Allah! Waye ne ka nada musu a matsayin khalifa a kansu?’, sai yace: ‘Mai gyaran takalmi’. Duk sai muka je waje muka duba sai muka ga Ali ne, sai kika ce: ‘Ya ma’aikin Allah, banga kowa ba fa sai Ali’, sai yace: ‘Ai shi ne”. A’isha tace: “Na tuna wannan ma”. Sannan sai Ummu Salma tace mata: “To bayan kin san wadannan duka me zai sa kije (yakan Ali)?”, sai tace: “Na fito ne domin in sulhunta tsakanin mutane”. Sai Ummu salma taci gaba da kokarin hanata zuwa yakan Imam Ali (AS) tana ce mata: “In ginshikan musulunci sun lonkoshe, ba mata ne zasu mikar da su ba, kuma in sun tsage ba mata ne zasu hada su ba, babban abinda ya kamanci mata shine su takaita ganinsu kuma su kare mutuncinsu. Meye zaki ce in Manzon Allah (S) ya bayyana a gareki a hany`an ki (na zuwa yakin) ya sameki kina haye a bayan rakumi kuna tafiya? Wallahi in da ni aka sa a wannan tafiyan naki (na zuwa yaki) sannan ace min in shiga aljanna, to da zan ji kun`yan fuskantan Muhammad (S) bayan na kawar da duk hijaban da yasa min”. Ban da Ummu Salma, dan `yar uwarta Zaid bin Sauhan shima yayi kokarin ya hanata lokacin da ta tura masa wasika bayan ta iso Basra tana cewa: “Daga A’isha uwar muminai, `yar Abubakar mai gaskiya, matar Annabi (S), zuwa ga dan da nake kauna Zaid Ibn Sauhan, (ina umurtanka da) ka kasance a gida, kasa mutane su kyamaci dan Abu Dalib. Ina kuma fatan jin abinda nake so daga gareka, domin kai kana daga cikin masu gaskiya a danginmu..wassalam”. Sai shi kuma ya tura mata amsa da cewa: “Daga Zaid Ibn Sauhan zuwa ga A’isha `yar Abubakar, Allah yayi umurni a gareku (mata), kuma yayi umurni a garemu (maza). Allah ya umurce ku da ku zauna a gidajenku, mu kuma ya umurce mu da muyi yaki. Wasikan ki ta sameni tana umurtana da aikata sabanin abinda Allah ya umurce ni da shi, kina umurta na da in`yi abinda Allah yace ku (mata) kuyi, kuma ke kina aikata abinda Allah yace in`yi! Umurninki (wani abu ne da) ba zan aikata shi ba, saboda haka ba wani amsa takamamme game da wasikan ki”. Kuma shi kansa Imam Ali (AS) yayi ta musu nasiha a Basaran akan hadarin dake cikin yakin amma abin ya faskara. Nisa’i ya nakalto, haka ma Hakim ya nakalto a Mustadrak cewa Sha’abi ya ruwaito daga Muslim bin Abi Bakra shi kuma daga babansa cewa: “Lokacin da Dalha da Zubair suka iso Basra, sai na dauki takobina da nufin inje in taimakesu. Sai naje gun da A’isha take, sai na samu tana cewa ayi wannan a bar wannan, tana ta bada umurni. Sai na tuna hadisin Manzon Allah (S) wanda nake yawan ji yana cewa: ‘Duk mutanen da mace ta shugabance su, ba zasu taba nasara ba’, sai kawai na fasa na koma”. Haka dai yaki ya balle, wanda ya jawo asaran rayukan musulmai dubbai da dama. A karshe, kamar yadda aka saba, Imam Ali (AS) yayi nasara a kansu; ya kuma yi yekuwar afuwa ga kowa, ya komar da Ummul Mumina A’isha zuwa Madina yana mai tunatar da ita horon Allah gareta na cewa: “Ku zauna a gidajenku, kuma kar ku rinka fita irin fitar jahiliyya” (Ahzab aya na 33).
Posted on: Fri, 20 Sep 2013 20:51:08 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015