Tambaya Ta Huxu Mene ne dangatakar addininku da harshen - TopicsExpress



          

Tambaya Ta Huxu Mene ne dangatakar addininku da harshen Farisanci? Domin mun lura cewa, harshen larabci ba shi da wata qima a wurin ku. Kuna fifita Farisanci da Farisawa akan ko wane harshe da ko waxanne irin mutane. Kafin ku yi gardama bari in bada ‘yan misalai don bayyana abin da nike nufi; Littafanku suna nuna cewa, Mahadinku, idan ya bayyana, zai halaka quraishawa, ya karkashe larabawa. Sannan daga cikin sunayensa akwai Khisru Majus Sarkin Majusawa! Daman kuma kun ce, Kisran Farisa wanda ya yaga wasiqar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama don cin mutunci zai shiga wuta amma an haramta ta akan sa. Littafanku suna nuna muhimmancin Salmanul Farisi akan kusan duk Sahabbai. Abu lu’luata, bamajusen da ya kashe Umar kuna girmama shi, kuna ziyartar qabarinsa. Al Gharithi ma a cikin gabatarwar littafinsa Aqdud Durar Fi Baqri Baxni Umar cewa ya yi, Abu Lu’ulu’ata ya cancanci rahama duk da kasancewar sa ba musulmi ba. Kuma ziyarar qabarinsa da yi masa addu’a na daga cikin mafi girman ayyukan lada saboda muhimmancin aikin da ya yi na kashe sayyidina Umar, surukin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama! Duba yadda Al-Ahqaqi a cikin littafinsa Risalatul Islam shafi na 324 yake kuka akan wai, qazamai, shaixanai, macuta – a cewar sa – suka yi wa tsarkakakkun ‘yan matan Farisa (majusawa) a lokacin da aka buxa ta. Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama fa kenan! Karbala kuma ta cikin Farisa tafi birnin Makka da na Madina daraja a wurin ku. Har ma darajar Ka’aba idan aka kwatanta ta da darajar Karbala kamar abin da allura zata xebo ne in aka tsoma ta a cikin teku. In ji Majlisi a Biharul Anwar (98/106). Bugu da qari kuma qasar Iran a yau, harshen da ta yarda da shi shi ne Farisanci kamar yadda ya zo a tsarin mulkinta. Wannan kuma ba zai bada mamaki ba in aka san cewa, mafi yawan Marji’an Shi’ah waxanda su ne mujtahidai masu bada fatawa a mataki na duniya duk bobayi ne; basu jin larabci. Irin su: Khumaini da Khamene’i da Rafsanjani da Khatami. Kai! Har da Sistani Sayyidul Muhaqqina na wannan zamani a wurin su! A shekarun baya ne tashar AlJazeerah ta yi wata fira da jagoran Shi’ah na Najeriya, sai ga shi ana fassara masa larabcin don ya bada amsa da turanci! Ko ba a lura ba?!!! Sai na ce, to, ai shi larabcin Aljazeerah ana yin sa ne da wasali! Ko ba a lura ba?!!!
Posted on: Tue, 09 Jul 2013 07:17:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015