UWA TA GARI GA DA NA GARI, Kai amma wannan Miji ya - TopicsExpress



          

UWA TA GARI GA DA NA GARI, Kai amma wannan Miji ya MORE.... Babban Daraktan Ilimi ne ya kai ziyara wata Makarantar Firamare don ziyarar aiki, sai ya shiga wani aji na kananan yara, daga nan ya fara tambayar yara sunayensu da kuma me suke so su zama idan su kammala karatu, wani ya ce Likita wani Engr wani Gwamna wani Shugaban kasa, ko da ya tambayi wani yaro sai ya ce shi burin shi ya zama SAHABIN Annabi (saw). Wannan buri na yaro ya ja hankalin Darakta da yan rakiyarsa sosai. Bayan tafiyar Darakta sai malamin yaran nan ya kira yaron ya tambaye shi; Me yasa kake son zama Sahabin Annabi (saw)? Sai yaron ya ba shi amsa da cewa: Kullum da dare kafin muyi bacci mamanmu takan bamu tarihin sahabban Annabi (saw), jarumtar su da hidimarsu ga Annabi (saw) da Addini. Anan malamin ya fahimci lalle wannan yaro ya dace da uwa tagari, don bata bar yayanta gaban akwatin talabijin ba balle su kwace mata su.... Allah ya azurtamu da mataye nagari, ameen.
Posted on: Sat, 19 Oct 2013 09:58:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015