WASU DAGA CIKIN HAKKOKIN MIJI AKAN MATARSA. 1-Soyayya ta - TopicsExpress



          

WASU DAGA CIKIN HAKKOKIN MIJI AKAN MATARSA. 1-Soyayya ta gaskiya. 2-Tsare Amana Miji. 3-Tausasawa miji da wasa dadariya dashi. 4-Tsare sirrin miji. 5-Kada ta fita daga gidansa sai da izininsa. 6-Baza tayi azumin nafila ba sai da izininsa. 7-Ta yarda ya sadu da ita duklokacin da yake bukata, dan Annabi Mai tsira aminci yace duk matar da taki mijinta ya sadu da ita a duk lokacin da yake so, to Malaiku zasuyi ta laantar ta bazasu su daina ba har sai lokacin da ta yardada shi. (BUKHARI/ MUSLIM). 8-Ta saurari mijinta kuma tayi masa biyayya matukar baaikin laifi ya umurceta dayi ba. 9-Mace ta nisanci raina abin da mijinta ya bata, domin Annabi muhammad mai tsira aminci yace Mata zasu shiga wuta ne saboda kafurce wa mazajensu, wato raina alherin miji (BUKHARI/ MUSLIM) 10-Kada mace ta cutar da mijinta da magana ko da aiki. 11-Mace tayi ado da kwalliya wa mijinta, saboda Annabi mai tsira da aminci yaceAllah kyakkyawa ne, kuma yana son kyakkyawan abubuwa, (IMAM MUSLIM YA RUWAITO) 12-Mace ta tsare dukiyar mijinta dana yayansa harmadana gidansa, dan Annabi mai tsira da aminci yaceMace mai kiwo ce a gidanta, zaa tambayeta abin da ta kiwata. 13-Mace tayi gaggawan baiwa mijinta hakuri a duk lokacin da taga yayi fushi, Tace masa, dan Allah kayi hakuri, bansan abin da nayi zai bata maka rai ba, ka yafe mini dan girman Allah. 14-Mace tayiwa mijinta dukkan irin aikin da ake bukata ayishi a gida. 15-Mace ta kyautata halayenta ga iyalan mijinta. 16-Mace kada tayi abokantaka da mugayen kawaye, sai su hallakar dake baki sani ba. 17-Mace ta zama mai tausayawa mijinta, kamar yadda uwa take tausayin Danta. 18-Mace ta zama mai Biyayya ga mijinta. 19-Mace ta zama Abokiyar rayuwa ga mijinta. 20-Mace ta kusanci dukkan abin da mijinta yake so. 21-Mace ta nisanci dukkan abin da mijinta yake ki 22-Kiyi murmushi a duk sanda mijinki ya kalleki. 23-Kiyi masa addua a duk lokacin da zai fita, kice adawo lafiya Allah ya bada saa. 24-Kiyi masa addua kuma a duk lokacin da bakya ganinsabayan bayanan. 25-Idan mijinki ya dawo ki karbi abin hannunsa, tare da yi masa sannu da zuwa, dan girmama shi. 26- A duk samda zakiyi magana da mijinki ki gaya masa magana mai dadi, mai tabshi, kada ki daga muryanki akan nasa, kuma kada ki masa tsawa har ki harare shi. 27-Ki zama cikin tsabta da kamshi mai dadi duk lokacin da kuke tare. 28-Ki sanya hijabi a duk lokacin da kuke tare da wadanda ba muharramanki ba. 29-Kisa lokaci idonki, ki kumashafa jan baki, kuma ki shafa turare, amma sai kuna tare dashi a gida dan mace bata shafa turare ko janbaki ta fitaanguwa dashi. 30-Ki kaskantar da kai dan biyayya a gare shi. 31-Ki san lokacin da yake dawowa dan kada ya sameki a cikin kazanta, ki kuma san lokacin cin abincin sa dan ki tanada ba sai yazo yana nema ba. 32-Bayan kin gama masa komi ki tambaye shi ko yana da wata bukata a gareki, dan mi biya masa ita. 33-Kar ki nuna murnan ki idan wata hasara ta same shi,ki nuna masa kamar kece kika yi hasarsar. 34-hakanan kiyi murna da duk wani alherin daya samu. 35-Ki zama kamar matan sahabbai, yadda sukewa mazajensu. Idan miji zai fita sai suce a dawo lafiya, kar ka kawo mana haram zamu iya hakuri da yunwar duniya, amma baza mu iya hakuri da azaba ba gobe lahira. In ya dawo kuma su karbeshi, suyi Masa sannu da zuwa suce masa yau wace aya ne ta sauka kuma wane hadithi manzon Allah mai tsira da aminci ya fada. In dare yayi kuma sai tayi wanka, ta zabi tufan da yafi kyau ta rangada ado, ta fuskanci mijinta tana tana faraa tana murmushi, tana ce masa kana da wata bukatane gareni? In kana da bukata ka biya. To ya ke yar uwa musulma, idan kina son tsira duniya da lahira ki kiyaye harkokin kuma kiyi aiki dasuidan ba haka kuma ki tuna ranar mutuwa da zaa saki cikin kabari ba taburma, ba katifa, ba gado, ba window, ba kofa,bama wata iska da zata sameki, daga ke sai halinki. A cikin kabari a doka miki tukwane a kanki a saka itatuwa a tattare, asa ganye adoddara, a kwaba kasa a lillike sannan a kawo sauran kasan data rage a rufe kabarin da kike ciki Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Idan kuma kina son Allah Taala ya yalwata, kuma ya haskaka, kuma kabarinki ya zama dausayin Aljannah to ki kiyaye wadannan harkokin mijinki a kanki domin Annabimai tsira da aminci yace da wata mace, Mijinki Aljannarki ko wutarki, ki duba kiga yaya matsayinki a wurin mijinki, kin tsare hakkokin sa ko baki tsare ba, idan kin tsare to ya zama aljannar ki kenan, (IMAM AHMAD YA RUWAITO KUMA ADAWI NE YA INGANTA HADITH DIN). Allah ya bamu ikon yin daidai a dukkan alamurran mu.
Posted on: Fri, 18 Oct 2013 04:49:26 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015