Wajen wani taro sai ake tambayar Mazajen wajen anya kuwa kuna son - TopicsExpress



          

Wajen wani taro sai ake tambayar Mazajen wajen anya kuwa kuna son Matanku??? Gaba daya suka amsa da kwarai kuwa,to a lokacin ne wanda yayi tambayar yasake cewa to yaushe rabon da kowannensu ya furtawa Matarsa cewa yana sonta,misali yace I love u. To anan ne suka fara bada amsa wani yace kusan wata guda kenan,wani yace fiyeda shekara,wani yace bazai iya tunawa ba da sauransu. Nan take wanda yayi musu tambayar yace to kowa ya rubuta sakonINA SONKIwato I love u,tawayar salula ya turawa Matarsa domin ganin wadanne irin amsoshi zasu bayar. Cikinkankanin lokaci kuwa saiga amsoshi sun fara zuwa daga wajen matayen nan,kuma a lokacin ne mai tambayar yabasu umarnin suyi musayar wayoyin domin a karanta amsar da Matar kowannensu ta bayar. Ga bayanin da MATAR kowannensu ta bayar; 1.Mhm,da kenan banda yanzu. 2.Maganar auren naka tarushe kenan. 3.Kana son nabaka aron kudi kenan. 4.Mhm,me kake nufi? Wannan karon bazan yarda ba. 5.A mafarki kenan. 6.Tam,Allah ya kamaka bari kadawo ka fadamin wadda ka aikawa wannan sakon. 7.Na fadama kadena shaye-shaye. 8.Waye wannan? 9.Wata sabuwa. 10.Yau kuma?
Posted on: Tue, 15 Oct 2013 21:35:47 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015