Wani attajiri ne yake wata kyauta a duk lokacin da sallar layya - TopicsExpress



          

Wani attajiri ne yake wata kyauta a duk lokacin da sallar layya taxo. Kyautar kuwa itace yakan sa a siyo mas raguna sai a kai bayan masallaci a boye su bayan an kare sallah sai ya mike. Yace waye mai tsoron allah a nan?. Sai wani mutum yace gani. Sai attajiri yace to taso. Da suka je bayan masallaci sai aka yanka rago aka baiwa mutumen nan yace jeka gida ka gyara. Sai ya dawo masallaci ya koma cewa ina wani mai tsoron allah a nan.yayi haka har sau uku. To a na hudu lokacin yaxo da wuka tsirara kuma jini yana xuba a jikinta. Sai yace ina wani mai tsoron allah sai kowa yayi shiru yace babu? Suka yi shiru. Kowa na tsoron yace gashi a tafi da shi a yanka tinda yatafi da mutane uku duk ba wanda ya dawo kuma gashi yaxo da wuka jike da jini. CAN Sai ladan yace AI IN DAI TSORON ALLAH NE TO GA SU LIMAN NAN. SAI Liman yace INJI UBANWA??? A ubanka nake da tsoran Allah, ni tsohon bamaguje ne!!! Hahahaha
Posted on: Wed, 02 Oct 2013 02:08:25 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015