Wani barawo ne ya hau babur din wani dan acaba, ashe ba shi da - TopicsExpress



          

Wani barawo ne ya hau babur din wani dan acaba, ashe ba shi da kudi, suna cikin tafiya sai da suka zo kusa da wata makabarta sai barawon ya ce da dan acaba, a nan zai sauka, domin shi fatalwa ne. Sai dan acaban ya bi shi cikin makabartar domin ya karbi kudinsa. Suna zuwa sai barawon ya ce wane idan kana cikin kabarin nan, ka ba ni Naira ashirin na biya dan acaba. To ashe bai sani ba, akwai wani mahaukaci a kwance a kusa da wani kabari, nan take mahaukacin ya amsa ya ce: “ga 50 kawo 20” Su biyun sai suka ruga a guje .kyal.kyal.kyal
Posted on: Wed, 09 Oct 2013 01:14:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015