YA ALLAH KA WARGAZA GWAMNATIN BOBO - TopicsExpress



          

YA ALLAH KA WARGAZA GWAMNATIN BOBO HARAM #BBC_HAUSA Rahotannin da ke fitowa daga garin Mubi da ke jihar Adamawa na nuna cewa yan kungiyar Boko Haram sun kame garin, har ma sunkafa tutarsu. Kazalika sun kafa dokar hana fita ko shiga garin, sannan a bangare guda kuma an datse layukan waya,lamarin da ya munana harkar sadarwa. Wani dan garin na Mubi, Mallam Ahmed Sajo ya shaidawa BBC cewar lamarin ya ritsa da yarsa dakuma iyayensa, wadanda ya ce ya daina jin duriyarsu.Malam Sajo ya ce Wadannan mutanen sun kama garin, sun fasa kofar fursuna sun saki fursunoni. Sun kuma kama barikin yan sandasannan sun hana mutane shigowa ko barin garin. Ya kara da cewar Galibin jamaar garin sun gudu. Yan Boko Haram suna yawo da motoci da babura a cikin garin suna ta kabbara. Muzauna garin da dama sun bazama daji da tsaunuka don neman tsira. Kawo yanzu hukumomi a Nigeria ba su ce komai ba game da lamarin.Garin Mubi wanda ke kusa da iyaka da Kamaru shi ne gari na biyu mafi girma a jihar Adamawa. A farkon watan nan, gwamnatin Nigeria ta sanar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da yan BokoHaram, abin da zai kai ga sakin yan matan Chibok su sama da 200da yan Boko Haram din suka sace sama da watanni shida. Allah kasaukar da balain ka akan duk mai hannu akan cusgunawa bayin ka da kashe su Allh ka bi mana kadi ya Allah
Posted on: Wed, 29 Oct 2014 20:26:32 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015