YADDA TA KARE TSAKANIN MUHAMMAD ABUBAKAR DA DAN USTAZU (2) - TopicsExpress



          

YADDA TA KARE TSAKANIN MUHAMMAD ABUBAKAR DA DAN USTAZU (2) (Karshen Labari) Shi dai dan Ustazu, yanda siffar sa take yanayi ne irin na Ustazai kamar yadda kowa yasan siffar Ustazai take. Budar bakin da Ustazu zai yi sai kawai shima ya marawa mutanen motar nan baya, Ustazu ya fara fada a cikin mota shi dai bai kama suna ba amma yana gugar zana, ya fara surutu shi kadai kawai mutane basu fahimci Hadisi ba sai su zo suyi ta aiki dashi bata hanyar da ta dace ba, suma lokacin Sahabbai ai tafiya suke mai nisan gaske suyi tafiya kimanin kilomita dari biyar a cikin Sahara, ga wahala ga waye ga waye shi yasa aka rangwanta musu, amma kawai kai ka tashi ‘yar tafiya nan da nan sai ka ajje azumi. Shi yasa ake so mutane su samu malamai masu ilimi amma ba Malaman da suma basu gama fahimtar Addini ba. Duk wannan Magana da Ustazu yake Muhammad bai tanka masa ba, shi dai kawai ya sa Dan Biju Milk din sa da Biscuit yana ci. Can an jima bayan Ustazu ya gama fadan sa har mota tayi shiru sai kawai aka ga Muhammad ya mika hannu cikin Boot na mota ya dauko wata jaka, menene kuma haka? Ashe Muhammad ba jahili bane wata jakar littattafan sa ce na Bangaren addini ya dauko, tunda y agama Informatics shine ya tattaro kayan sa gaba daya ya taho dasu gida. Nan fa ya fara futo da littattafai har guda Hudu, sai yace Driver don Allah ina so a bani dama zan dan karonto wani abu a cikin littattafan nan, Driver yace an baka dama. Muhammad ya bude daya daga cikin littafin nan ya fara karonto hujjar da ta bashi dama ya sha azumi yayin da yake a matsayin matafiyi, yana gama karanto hujjojin littafin farko sai ya rufe, ya tambayi Driver, Driver an bani dama na karanto wani? Driver yace an baka dama. Ya dauko na biyu ya karonto wani kaso daga ciki, haka yayi har sai da ya gama karonto littattafan nan guda hudu. Bai ce da dan Ustazu kala ba, daga nan kuma ‘yan mota sai suka koma kan Dan Ustazu, kawai kai Malam dama ba wata hujja ce da kai ba amma kayi ta fada, ashe kaine ma baka fahimci addinin ba. Haka dai suka yi ta cashewa Dan Ustazu, shi kuma gaba daya kunya ta kama shi bai iya cewa uffan ba. Wannan shine abin da ya wakana tsakanin Muhammad Abubakar da Dan Ustazu. Insha Allahu idan na samu lokaci zan kawo abubuwan da suke bawa mutum damar kin yin Azumi a watan Ramadan. Sau da yawa mukan wahalar da kan mu akan abin da Allah yayi mana rangwame. Annabi kuma yace “Allah yana so idan yayiwa bawa sauki, to ya karbi wannan saukin”. Allah ka bamu ilimi wanda zamu ke aiki da shi, ba ilimi na ji ka karkade kunne ba. Ameen thumma ameen
Posted on: Mon, 19 Aug 2013 12:18:47 +0000

Trending Topics



v>

Recently Viewed Topics




© 2015