ZINA DA ILLOLINTA ZINA zina ita ce saduwar namiji da mace - TopicsExpress



          

ZINA DA ILLOLINTA ZINA zina ita ce saduwar namiji da mace ba tare da aure ba,bisa yarda mace.wannan saduwa haramun ce.Allah yana cewa (mazinaciya da mazinaci ku yi musu bulala dari kowannansu)wannan hukuncin su marasa aure kenan.masu aure kuma hukunci jefewa ne a kan su.Yazo a hadisi cewa:kada kuyi Zina da matan wasu domin kada a yi da matanku ILLOLIN ZINA. A)fuskantar fushin Allah idai baa tuba ba B)zubewar mutuncin junansu da kuma wadanda suka san sun aikata haka. C)QeQashewar zuciya da zai haifar da rashin kunya da tsoran Allah,da rashin ganin Qimar sabon D)Lalata tarbiyyar Alumma da yadan fasadi.ba abin da yake saurin Lalata tarbiyyar Alumma cikin gaggawa irin zina.*manzo Allah(s.a.w)yana cewaAllah ya haramta zina saboda abin da take haifarwa na barna tana jawo kisan kai da rashin adalci da rashin tarbiyya E) Tana jawo talauci da fatara a cikin Alumma F) tana haifar da miyagun cututtuka a cikin Alumma misali cutar HIV (AIDS)da sauransu,Manzo Allah yana cewa,idan zina tayi yawa a Qarshen duniya sai ake mutuwa bagatatan(farat daya) G)Zubar da darajar aure misali duk mazinaci da mazinaciya basa ganin darajar aure H) kashe dandanon maauranta.ita zina tana hana wa mai yin ta jin dadin matarsa ta gida ko mijinta na gida.shi yasa ma manzo Allah (s)yake cewa.kada ku yi zina sa ta gusar muku da dandanon matanku da kamun kansu I) Samar da yaya shegu marasa uba cikin Alumma daga bisani su zama miyagun cikin Alumma sakamako rashin tsarkinsu da rashin mai tarbiyantarwa.ita zina bata aukowa sai mace ta yarda ta kuma aminci in kuma har kuma zinar ta kasance tsakanin su ta tafi kowa shiga balai da jin kunya da zubar da mutumcin zuriyar ta.... YA Allah muna tawassali da kyawawan sunayenka kamana tsari daga aikata zina,masuyi kuma Allah ka shiryesu,idan sun qi bari Allah kai kasan yadda zakai dasu...
Posted on: Sun, 12 Jan 2014 07:49:12 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015