ZIYARA TA MUSAMMAN Kwamitin social media Borno state, tare da - TopicsExpress



          

ZIYARA TA MUSAMMAN Kwamitin social media Borno state, tare da hadin gwuiwar majalisar agaji sun kai ziyara ga wasu daga cikin iyaye, malamai da kuma shuwagabannin kungiya. Tawagar kar kashin jagorancin STATE DIRECTOR (Muhammad Lawan) Ta shirya wannan ziyarar ne domin karadankon zumunci da kuma kyakykyar alaka tsakanin ta da sauran bangarorin kungiya (majalisar zartarwa da ta malamai). A yayin ziyarar, tawagar ta baiyan farincikin ta dangane da muhimmiyar rawa da shuwagabanni suke takawa wajen ciyar da wannan kungiya. Sai dai tawagar ta nuna damuwa kan yadda wasun su (shuwagabbani) ke maida majalisar agaji saniyar ware. Da suke maida martani, shuwagabannin sun yi matukar jin dadi dangane da wannan ziyarar, sannan sun sha alwashin yin aiki tare kamar yadda aka saba kuma sun yi alkawarin kawo gyara ga dukkan abin da ya dace a gyara. Daga cikin wadanda tawagar ta ziyarta sun hada da 1.Sheikh Maina Abubakar 2.Alhaji Baffa Usman 3.Mal. Hassan Husaini 4.Alh.Adam Yahaya (national discipline) 5.Sheikh Gambo Kyari. Wannan ziyarar ta sami halartar daraktan jahar borno da yan majalisar shi, sakataren social media da membobin kwamitin.
Posted on: Mon, 20 Oct 2014 06:26:12 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015