ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta - TopicsExpress



          

ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 25 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam A Lokacin Samartaka 4. Aure Da Gina Iyali A daidai lokacin da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kai shekaru ashirin da biyar ya yi fice a wajen sadaukantaka da halin girma. Ba wani gida daga cikin gidajen Quraish face suna farin cikin in da zai nemi aure a gidansu. Ba kuma wata mace daga cikin su karama ce ko babba da ba zata yi murna ba idan aka ce Muhammad ne Sallallahu Alaihi Wasallam yake neman auren ta. A daidai wannan lokacin ne Sallallahu Alaihi Wasallam ya nemi aure. To, amma abin shaawa shi ne bai nemi auren karamar yarinya ba. Wacce ya nema ita ce khadijayar gidan Khuwailid, bazawarayar babban gida da ta yi aure har sau biyu kuma tana dayaya. As-Siratun Nabawiyyah, na Sallabi, shafi na 59-61. A game da dalilin aurensu, da yawan marubuta sun kawo labarin cewa, kasuwanci ne ya fara hada su in da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya je birnin Sham tare da bawanta Maisara suka yi fatauci da dukiyarta. Aka ce bayan da ta ga albarkokin wannan bawan Allah ne, da kanta sai ta nemi kulla zumuntar aure da shi kuma ta aiki kawarta Nafisah bint Munabbih wadda ta shirya ma sa maganar kuma ya amince da ita. Asalin wannan ruwaya ta fito ne daga littafin shaihun malamin nan Ibnu Ishaq amma fa ba ta da isnadi. Don haka malamai ba su karfafa ta ba. Shi kam zancen auren tabbatacce ne har a mafi ingancin littafan ruwaya na Bukhari da Muslim. Babu wani sabani cewa, shekarun manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a lokacin auren 25 ne. Amma game da shekarun amaryar tasa ruwayoyi sun yi sabani. A lokacin da fitaccen malamin nan Waqidi yake ganin ta kai shekaru 40, shi kuma malam Ibnu Ishaq na ganin shekarunta 28 ne. Wannan kauli nasa kuwa babu shakka ya fi karfi. Domin ko bayan kasancewar malamai na da shakku wajen karbar kaulin Waqidi, maganar Ibnu Ishaq ta fi kusa da hankali. Domin kuwa mawuyacin abu ne - a aladance - macen da ta kai shekaru 40 ta haifiyaya 6 bayan haka. A bisa wannan riwayar kenan Nana Khadija ta girme shi ne da shekaru 3. Kuma dukyayan da Allah ya ba shi ita ce ta haife su in ban da Ibrahim wanda kuyangarsa Mariyayan asalin kasar Masar ta haifa. A cikin ikon Allah kuwayayan nasa gaba daya sun riga shi komawa ga Allah in ban dayar aurtanyaya matansa; ita ce sayyida Fatima. Ita kam ta rayu dan lokaci kadan da bai shige wata shida ba a bayansa. Duba: Rasulullahi Fi Makka, shafi na 79. Nana Khadija macce ce mai hakuri da kaifin hankali da sanin ya kamata. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da kansa ya kan nemi shawararta a wasu alamurra nasa. Kuma babu shakka cewa, ya ji dadin zama da ita fiye da yadda za a misalta. Bayan so da kauna da ke tsakanin su Nana Khadija ta taimaki maigidanta matuka a lokacin da bai da wata madafa in ba tata ba. Shi ya sa ma bai taba tunanin kara aure ba duk tsawon rayuwarta. Sun yi shekaru 21 tare da ita sannan Allah ya karbi ranta. Kuma yakan fadi alherinta ko bayan mutuwar ta har a gaban iyalansa. Abin da Nana Aisha ta ce ya kan motsa kishi a zuciyarta amma ba yadda za ta yi domin manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam mutum ne da ba ya manta alheri ko kankane ne aka yi ma sa ballantana kuma alherin babbar masoyiyarsa uwaryayansa. Sahihu Muslim, Kitab Fadhail As-Sahaba, hadisi na 2437. Babu shakka wannan uwa ta mummunai ta karantar da mu abubuwa da dama. Kuma a dalilin aurenta alummar musulmi sun karanci darussa da hukunce hukunce masu amfani. Da farko dai mun gano cewa, halas ne ga namiji ya auri matar da ta girme shi, ita ma halas ne ta auri wanda bai kai shekarunta ba. Sannan halas ne mace ta nuna kanta ga mutumin kirki don neman ya aure ta. Kuma ya halasta namiji ya tare da matarsa a gidanta idan shi bai mallaki gida ba. Mun kuma fahimci cewa, auren macce mawadaciya ga namiji talaka ba laifi ba ne kuma ba aibi ba matukar akwai so da kauna da mutuntawa. Idan ma har ta taimaka bisa radin kanta ta dauke ma sa wasu nauye-nauyen gida da kudinta kuma a haka ta kyautata ba ta yi laifi ba. Macce kuma - bisa ga darasin da Nana Khadija ta koya ma alumma - ita ce babban jigon da namiji managarci. Shi ya sa masu hikima ke cewa, duk in da ka ga namiji ya gawurta akwai nagartacciyar macce a bayansa. Ar-Rahmah Al-Muhdah, na Sheikh Dr. Ali Muhammad As-Sheikh, shafi na 98. Nana Khadija dai ba wani mahaluki da manzon girma ya amfana da shi a farkon rayuwarsa ta addini kamar ta. Shi ya sa da aka tambayi shehin musulunci Ibnu Taimiyyah game da matsayinta da na kanwarta uwar mummunai Aisha sai ya sa hikima, ya ce, a farkon musulunci Khadija ita ce mafificiyar macce wacce ta taimaki manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ta hanyar karfafa shi da taimakon daawarsa. A karshen musulunci kuma Nana Aisha ita ce mafificiya wacce ta kiyaye ma musulmi kaffatanin rayuwar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da irin basirar da Allah ya ba ta. Har ya zama ba wani hukunci da ya danganci rayuwarsa face an samo wani ilmi mai albarka dangane da shi a wurin ta. Babban darasi ga malamai magadan annabawa a cikin wannan lamari shi ne su rinka taka-tsantsan wajen neman aure. A maimakon kyau da kuruciya su nemi asuli da tarbiyya da nagarta. A cikin mutuwaryayan manzon Allah tun a rayuwarsa akwai darasi babba. Manzon Allah ya dandani zafin mutuwarsu kamar yadda ya dandani zafin mutuwar iyayensa tun da wuri. Haka ita ma uwar tasu manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya dandani zafin mutuwar ta wacce ta zo daidai da mutuwar baffansa mai kyautata kula da shi da ba shi kariya daga makiya. Kada ka taba tsammanin idan kana masoyin Allah ba zaka gamu da matsalolin rayuwa ba. Ai duniya ba komai ba ce a wurin Allah. Kuma jarabawoyin rayuwa sukan kara ma mumini kaifin hankali da sabawa da hakuri da tausaya ma jamaa kamar yadda jin dadin duniya idan ya yi yawa yake sa dakilewar basira da karancin hakuri da raina mutane. Ga kuma dinbin lada da Allah ya yi tanadi ga wanda ya yi hakuri da dacin rayuwa ya mayar da alamari ga Allah. Wani muhimmin darasi kuma a nan shi ne, lura da cewa, addinin musulunci ba kayan gado ba ne. Domin kuwa da haka ne abu ne mai sauki ga madaukakin sarki ya raya ma manzoyayansa maza domin su gaje shi. Allah dai ya yi ma sa niimar haifuwa, bai zamo bakarariya ba. Ya jiyar da shi dadin haifuwa na wani lokaci sannan ya karbi abinsa. A cikin wannan akwai sanyayawa ga wanda aka ba shi aka amshe, ko kuma wanda ba a ba shi ba ma sam. Sai su yi koyi da maaiki Sallallahu Alaihi Wasallam a cikin hakurinsa da juriya.
Posted on: Sun, 01 Dec 2013 18:47:17 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015