Abubakar Ibrahim yarubuta..... KHUTBAN MAULANA SHEIK - TopicsExpress



          

Abubakar Ibrahim yarubuta..... KHUTBAN MAULANA SHEIK DAHIRU BAUCHI A BABBAN MASALLACINSA DAKE GARIN BAUCHI! shehu yaja hankalin musulmin duniya akan muhimmancin hadin kai,yace da hadinkai ake samun dukkan nasarori, amma dole akwai sharadi, A yadda da musuluncin kowa matuqan yana sallah, yana tauhidi, kuma a sallama ma wanda yafi ilimi, yace bayan yadawo daga qasa mai tsarki yaji labari wai ance dariqa ta hade da izala yace wannan magana qaryace, yace, ba hadewa mukayiba mun hadu dai,yace idan suna so a hade su dawo gida inda suke, dama su suka tafi suka barmu, in sun dawo sun bimu sallah sunci yankanmu,shi kenan, shehu yace ana zaune lafiya wajan 1958 zuwa 1959, babban malaminsu Abubakar gumi, ya rubuta wani littafi mai suna Alanwaru rahamaniyya fil hidayatul firqatu Tijjaniyya,acikin littafin yace yan Tijjaniyya kafiraine, yace yan qadiriya ma kafiraine, yasakece musulmin da baya kodaya daga ciki kafircinsa yafi nakowa, to yaya zaa zauna lafiya, bayan ka kafirta kowa, yace ba ruwanmu da izala, ya kuma ce muriqi zikiriri da kyau.
Posted on: Fri, 25 Oct 2013 14:35:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015