Assalamu alaikum. Neman Shawara dan Allah karku bada sunana. Ina - TopicsExpress



          

Assalamu alaikum. Neman Shawara dan Allah karku bada sunana. Ina da friends a facebook, sai naga kullun suna cmmnt a wannan shafi, sai nace bari na duba na gani, na. Shigo na duba, naga irin shawarar da mutane suke bayarwa, hakan yasa nake so. Na fada muku abun da yake damuna, kuma na kasa gaya. Ma kowa. Ni dai dan kasuwa ne, ina garin Lafia, na tashi a cikin rayuwa ta kunci, Allah ya jarabceni d a talauci, akwai lokacin da bana ma cin abinci, tsabar rashi, cikin ikon Allah sai na hadu da wani bawan Allah, da yaga bani da abunyi, sai ya ce yana da shago na sai da kaya, nima in zo in dunga duba mai kaya, kasancewa wajen babba ne, akwai yaran aiki irin na dayawa. Muka shaku dashi, cikin lokaci kadan, har yafara tura ni, ina zuwa kano dauko kaya, ya yarda dani, bayan munyi shekaru, ranar ya kirani ya mun albishir, akan ya bude mun shago, ya mallaka mun, bayan nan Sai Allah ya buda mun, har na bude rumfuna, daga baya har na fara fita waje da kaina, kawo kaya, toh mai gidana akwai yarinyarshi da yake sonta sosai, ita kadai ce ya haifa. jinin mu ya hadu da ita, ana cikin haka soyayya ta kullu, kasancewa babanta ya sanni, cikin lokaci kalilan mukayi aure, yanzu Allah ya azurta mu da yaya 2. Yan uwa ina so ku nutsu kuji abun da zan gaya muku, ita dai matannan tawa, irin rayuwar da take, kullun tana BB chat, ko facebook, kuma a matsayinta na matar aure, duk da dai tace mun tana magana da abokanta ne, kamar yarda nake, amma abun da yake damuna, sai naji ta na magana da maza, bata yarda na taba wayarta, in na tambayeta sai tace abokanta ne, nasha dawo gida sai naga Kato a gida na, ko acemun an ganta a motar wani, kuma nima nasha ganinta, na mata fada akan wannan amma taki ji, har hakan yasa na fara, tunanin meye alakarta da maza tana matar aure? Kuma ina suke zuwa? kuma ina jin nauyin mahaifinta, ban san tukararshi da wannan maganar, ni kuma abun ya dameni, ina ta kai kukana ga ubangijina. Sai dai wani abu daya. Apart from that, tana da kirki, matsalarta kawai, bata ji, sai abun da taso yi, ku bani shawara, tare da sani a cikin adduoinku Daga Imran Musa Jahun
Posted on: Sat, 23 Nov 2013 05:32:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015