BA MAGE BA MIYAU *****************************Rahotannin dake - TopicsExpress



          

BA MAGE BA MIYAU *****************************Rahotannin dake ishe mu daga gidan gwamnatin kano shine MADUGUN JAR HULA YA NUNA #BANDIRAWO A MATSAYIN DAN TAKARARSA SANNAN #GAWUNA MATAIMAKINSA. Hakika wannan kakabe ko kadan bai bani mamaki ba domin nasan daukacin kanawa sun san cewa dukkan aika aikar da madugu yake tafkawa da shi da bandirawo suke tafkata. Da zaku taya ni lissafi ni kuma da na saka ku akan hanya. 1.sanarwar goyon bayan janye tallafin man fetur Bandirawo ne ya shelantawa duniya. 2.sanarwar dokar hana goyo ita ma bandirawo ne ya shelanta. 3.sanarwar dokar hana hawa mashin daga shida na yammaci ita ma bandirawo ne ya shelanta. 4.Aika aikar kaiwa marigayi sarkin kano takardar kin amincewa da nadin wazirin kano ita ma bandirawo ne ya mikata. 5.Aika aikar shiga gida gida da tilastawa iyaye lallai sai anyiwa yayansu allurar polio ita ma bandirawo ne ke jagoranta 6.Rike kudaden kananan hukumomi da sunan tsantseni wanda hakan ya jawo tsayawar kasuwanci da walwala cik a kano Bandirawo ne kwamishinan kananan hukumomi kunga kenan dashi ake kullawa. 7.kai in takaice muku zance dai kirkiro hukumar #kwarota da daure musu gindi suna cin zarafin alumma hakika da bandirawo ake kullawa. Don haka kanawa mu kula idan har kuka sake kuka zabi Bandirawo to tabbas mulkin maguzanci da sunan siyasa a kano bai kare ba. Allah ka tsare mu da mulkin yan jar hula. Ameeen.
Posted on: Fri, 28 Nov 2014 09:59:39 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015