Babu zaman da za a sake da sunan sulhunta Izala –Sheikh Jingir - TopicsExpress



          

Babu zaman da za a sake da sunan sulhunta Izala –Sheikh Jingir Category: Labarai Published on Friday, 16 August 2013 00:00 Written by Husaini Isah, Jos Hits: 777 Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Jingir ya ce babu wani sauran zama da za a sake da sunan wani sulhu a kungiyar domin kungiyar ta riga ta hade wuri daya. Ya ce “ wannan kungiya ta hade bayan da muka yi sulhu da junanmu, don haka babu wani sauran zama da zamu yi don yin wani sulhu. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga wata tawaga a karkashin jagorancin Mataimakinsa Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikun da suka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a garin Jos. Sheikh Jingir ya ce, “A lokacin hadewar da muka yi, babu wani mutum daga waje da ya zo ya hada mu, mu ne muka hadu da junanmu muka zauna muka yi sulhu. Kuma duk abubuwan da muka ajiye suna nan ba mu canja su ba, an ba kowa aiki a cikin tafiyar wannan kungiya, don haka mu yi hakuri da juna mu ci gaba da yin aiki. Mu je mu karfafa hadin kai a wannan kungiya da sauran al’ummar Musulmin kasar nan baki daya.” Dagan an sai ya bayyana cewa taron da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi da malaman addinin Musulunci na kasar nan a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura a kwanakin baya wata babbar nasara ce ga al’ummar Musulmin kasar nan. Ya ce a wannan zama tsakanin Shugaban kasa da malaman an tattauna matsalolin da suke damun Musulmin kasar nan. Don haka ya ce bai kamata wasu su rika suka kan taron ba. Sheikh Jingir ya yaba wa tawagar kan kaunar da suka nuna masa ta hanyar kawo masa ziyarar Barka da Sallah. Tunda farko a jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Malaman Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ne ya zauna da Shugaban kasa ya bayyana masa korafe-korafen al’ummar Musulmin kasar nan, musamman rashin adalcin da ake yi musu a jihohin Arewa. Ya ce kan wannan dalili Shugaban kasar ya ba sanata Ahmad Yarima dama ya zo da malaman addinin Musulunci su zauna da shi domin su tattauna wadannan koke-koke da suke damun Musulmi. Ya ce don haka aka tara malaman Musulunci 316 daga Arewa da Yamma da Kudancin kasar nan suka halarci wannan taro. Ya ce a wurin taron sun yi magana kan rufe layukan wayoyin waya da aka yi a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da maganar tsare Manjo Hamza Al-Mustapha da irin danniyar da ake yi wa al’ummar Musulmi a jihohin Yarbawa da matsalar Jihar Filato da sauransu. Ya ce a wurin taron Shugaban kasar ya yi alkawarin yin gyara tare da daukar matakai kan korafe-korafen al’ummar Musulmin. Ya ce tuni aka sake bude layukan wayoyi a jihohin Barno da Yobe da Adamawa kuma aka sako Manjo Al-Mustapha. Ya ce wadannan abubuwa su ne fa’idojin da aka samu a wurin taron da suka yi da Shugaban kasa. Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce a lokacin da marigayi Sheikh Abubakar Gumi yake raye an yi Shugaban kasa wanda ba Musulmi ba, kuma a lokacin idan ya kira marigayi Sheikh Gumi, don tatattaunawa kan wata matsala da take damun al’ummar Musulmi yakan tashi ya je ya samu Shugaban kasar su zauna. Ya ce don haka ya halatta idan Shugaban kasa Musulmi ne ko ba Musulmi ba ya kira malami kan wata matsala da take damun Musulmi, ya tafi ya zauna da shi, don a warware wannan matsala.
Posted on: Fri, 16 Aug 2013 20:39:49 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015