KIMA RAWANI A KAI: ALADA KO - TopicsExpress



          

KIMA RAWANI A KAI: ALADA KO SUNNAH???????????????????????? ALADA: shine abinda mutane suka gada kaka da kakanni wajen gudanar da wani alamari na rayuwa, (fassara daga encyclopedia britanica) sau tari aladar mutum tana nuna daga inda ya fito. Misalin alada, yanayin abinci, tufafi nauin bukukuwa da sauransu SUNNAH: kuma, shine abinda annabi ya aikata a aikace ko yayi umarni da aikatawa ko aka yi ya gani ko yaji amma bai hana ba. RAWANI: yana daga cikin tsohuwar aladar larabawa da hindu da farisa da kabilu da dama musamman da suke rayuwa inda hamada take. Annabi a matsayinsa na balarabe yana nada rawani da sauran tufafi na larabawan wancan lokacin kamar, kwarjalle, jubba, da hirami. Kenan rawani ya tabbata sunna tunda annabi ya kasance yana sawa dukda cewa aladar Larabawa ne. Sunna dai ta kasu kashi 3, akwai Sunnah Muakkada (itace sunna mai karfi sosai wacce barinta ma yana iya zama laifi) sai kuma Gaira Muakkada (itace sunna mustahabiya wacce barinta ba laifi bane amma aikata shi yafi muhimmanci), sai kuma kashi da karshe wato Sunna Adiyya (wannan bashi da karfi kwata kwata dan annabi ya aikata ne kawai a matsayin aladar larabawa) Abin lura shine annabi ba yazo ne akan kowa ya bar aladarsa ya kama ta larabawa ba. Abinda ake so kawai shine kar alada ta sabawa umarnin Musulinci. Ita kanta alada mai kyau wata aya ce ta Allah da zamu fahimci bambancin dake tsakanin mu. YA AYYUHAN NASI INNA KHALAQNAKUM MIN ZAKARIN WA UNSA WA JAALNAKUM SHUUBAN WA QABAILA LI TAARAFU... Dan haka yanzu idan Bahaushe yayi wankansa ya tsaftace kansa ya sanya rigarsa da wando ya kawo hularsa damanga ko zanna bukar ya kafa to daidai yake da mutumin daya kima rawani kuma mutumin daya kima rawani bai fishi lada ko falala dalilin rawanin ba sai dan INNA AKRAMAKUM INDALLAHI ATQAKUM. Dan haka ba a daukaka sunna adiyya akan aladar mutum mai kyau. Yana da kyau mutane susan inda ace mutum zai riki sunnah adiyya sau da kafa to da sai ya daina sa wando dan annabi SAW bai taba sa wando ba a rayuwar sa, lokacin sun kasance suna daura kwarjalle ne (har yanzu mutanen india da fakistan suna sawa) kuma ya koma amfani da jubba maimakon babbar riga ko alkyabba da muke gani malaman mu suna sawa sannan su rika rataya hirami ko daura shi a kugu dan wadannan duk aladar larabawan wancan lokacin ne kuma annabi ya kasance akansu ya rayu. Allah ya kara ganar damu gaskiya koda daga bakin makiyin mu ne kuma ya jagoranci zuciyar mu wajen yadda da ita da aiki da ita.
Posted on: Thu, 06 Mar 2014 19:06:43 +0000

Trending Topics



n-left:0px; min-height:30px;"> Below is the entire review of the book THE GORGEOUS NOTHINGS. This
Seattle Mariners Ichiro Suzuki Autographed / Signed Photo Full

Recently Viewed Topics




© 2015