KYAKKYAWAR DABIA annabi (s.a.w) yace babu abu dakesa maaunin - TopicsExpress



          

KYAKKYAWAR DABIA annabi (s.a.w) yace babu abu dakesa maaunin mumini yayi nauyi ranar kiyama sai kyawawan dabiu awani hadisin daban ya kuma cewa mafi soyuwarku gareni da kuma kusancin wajen zama ranar kiyama shine mai kyakkyawar dabia kuma antambayi manzon allah (s.a.w) menene mafi yawan abinda kesawa mutane su shiga aljanna yace tsoron allah da kuma kyakkyawan hali. Domin haka mafi kyawun dabia acikin jinsin bil adama shine annabi muhammad (s.a.w) kamar yadda allah (s.w.t) ya fada cikin (suratul kalam) lallai kai kana kan halayan kirki masu girma domin haka lokacin da aka turo (harsana bn sabit) kafin ya musulunta yayi masa zambo cikin waka da yazo gaban annabi sai yace mai kyakkyawar dabia kamarka tunda nake ban taba ganiba domin haka ubangiji yafada mana cikin (suratul ahzab) lallai cikin rayuwar manzon allah akwai abin koyi gareku mai kyau amma ga wanda ya yarda da allah da ranar lahira) saboda haka allah yasa muyi koyi da halayan annabi (s.a.w) domin mu zama masu kyawun halaye ameen
Posted on: Mon, 04 Nov 2013 14:36:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015