MATA YAUSHE ZAKU DAINA NEMAN DUNIYA?????????? Assalamu alaikum, - TopicsExpress



          

MATA YAUSHE ZAKU DAINA NEMAN DUNIYA?????????? Assalamu alaikum, maza da mata na wannan dandali da fatan kun wartsake lahiya. Yau zan dan yi wani tsokaci kadan game da wata tabargaza da mata da kuma wasu daga cikin mazaje ke goya musu baya keyi. .........................KARATU da AIKIN GWAMNATI shine mata suka dukufa wajen ganin cewa dole sai mazajen da suke soyayya dasu ko mazajensu na aure sun barsu sunyi. Idan kuka tsaya kuka lura zaku ga cewa wannan ba wani abu bane illa neman duniya da mata suka sanya a gaba. Saudayawa mata basa gabatar da irin wannan kuduri sai sun tabbatar da cewa sun mallake zuciyar abokin soyayyarsu. Ni kaina ta faru dani wallahi domin kuwa budurwata wadda nake buri na aura take fada mini cewa: “ITA FA SAI TAYI KARATU, KUMA SAI TAYI AIKIN GWAMNATI“!!! IDAN kaine aka gabatarwa da wannan kuduri wane mataki zaka dauka????????
Posted on: Fri, 22 Nov 2013 04:43:40 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015