Masu Sauraro Mustapha Muhammad ne ke muku fatan an wayi gari - TopicsExpress



          

Masu Sauraro Mustapha Muhammad ne ke muku fatan an wayi gari lafiya. A cikin shirin na mu na safiyar yau za ku ji martanin da wasu ke fadi kan harin bam da aka kai birnin Maiduguri, akwai kuma rahoto na musamman kan rufe iyakar Nijer da Algeriya da kuma Libiya. Haka zalika ana wani taro kan wahalar da alummar Syria ke sha na yunwa saboda yaki. Ku biyo mu don jin shirin mai kayatarwa wanda Badriyya Tijjani Kalarawi za ta gabatar insha Allah.
Posted on: Wed, 15 Jan 2014 04:27:29 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015