SABON ALAMARI Ban fiya son daukar kiran private number ba, - TopicsExpress



          

SABON ALAMARI Ban fiya son daukar kiran private number ba, saboda tsaro amma a wannan karon nayi mamaki dana tsinci dan yatsana yana yunkurin amsa kiran, a bari daya kuma ban hanashi ba dan zuciya ta aminta da na dauka. Hello, kana lafiya? dodon kunne na ya jiyo mun da amon muryar mace, na amsa a nutse; lafia lau nake, dan Allah lambar abokinka LAMARA ko lamro?? nake so, nayi murmushi nace any way LAMARA kike nufi, yes tace dani, na maida mata amsar da fadin yanzu ina tura wani movie a wayana, in na gama insha Allah zan turo miki amma da da zaki bude lambarki, ko flashing kin min kinga nayi miki text a layin, abin mamaki sai ji nayi tace nagode tunda wulaqanci zakai min, nagode tunda ka hanani lambar sai anjima ta kashe wayar kafin nace wani abu. Allah sarki, mata kenan basa tsaya su saurari bayani mudin abinda suke nema ya gaza samuwa a lokacin, na fadawa abokina Lamara bayan na bashi labarin abinda ya faru tsakanina da mai private number. Washe gari naje wajen mai aski na dan gyra gashi na, ina zaune ina sauraron faifan waqar Michael Jackson (billy jeans) wayana ta qara buga qugen tambarin kasata nigeria wanda shine kidan dake nuna ana kirana, na fiddo ta daga aljifuna, dubawar da zanyi sai naga private number, na dauka nayi sallama, ta amsa min amma wannan karan ta sanyaya muryarta, a raina nace tofa yau kuma da wane ta zo, kafin ta qara magana nace da ita bara na baki lambar Lamara din, abin mamaki tace dani tsaya prince wannan kiran ba irin waccan bane, ba kuma lambar kowa nake so ba, in ma ka ban lambar ba inda zan rubuta. Nace mata toh!tayi dariya tace dani amma ka ban mamaki, ni nasan sunanka kai baka sani ba, ka kuma ki tambayar sunana, nayi murmushi nace da ita ai na san sunanki mrs private number na kashe wayar. Baa fi minti 2 ta qara tace dani mai kace sunana, na amsa mata da Mrs Private Number, tayi dariya tace lallai kam, ni dai sunana Zainab, kuma maabociyar karanta Post ne a wannan dandalin amma bazan fadama garin mu ko lambar wayana ba, don kunyarka nake ji, Allah sarki kunya sai kace wani siriiki nace da ita, wallahi haka kurum naji ina jin kunyarka ta fada min muryarta qasa_qasa. To kaji ina daf da gama rubutun nan sai wani kira ya shigo, abun mamaki kiranta shima da Private Number, hmm wai ta kira kurum ta gaisheni Mai karatu shin wane irin kunyata ce wannan? Kai nifa na kasa gane wannan alamrin ko zaku iya ganar dani? #Prince_Ahmad_Amoeva 2B0EEE99 08066038946 Admin: #Lamara_Ibrahim Gamawa BBM- 22B3BE4F 08037436810
Posted on: Wed, 04 Dec 2013 20:08:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015