shin yankin niger delta suma suna fama da rashin wutan lantarki - TopicsExpress



          

shin yankin niger delta suma suna fama da rashin wutan lantarki kamar ningi jahar bauchi? Mutanen garin Ningi a Jihar Bauchi sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu da yadda aka shafe watanni 6 babu wutar lantarki a garin. Akasarin wadanda suka yi wannan zanga- zangar sun ce wannan lamarin ya nakkasa ayyukan da suka dogara kan wutar lantarki, kamar masu aikin welda da sayar da kayayyakin sanyi na firij. Mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, yace bai kamata a ce wannan lamarin ya gagari hukuma ba domin wadanda hakkin samar da wutar ke kansu ba su karfin ita hukuma ba. Sai dai kuma manajan hukumar wutar lantarkin mai kula da garin Ningi, yace sun samu umurnin cewa su mayarda layin wutar dake zuwa Ningi ya koma daga Bauchi, fadar Jihar, maimakon daga garin Birnin Kudu na Jihar Jigawa inda ake dauko wutar yanzu. Yace tun lokacin da aka mayar da hanyar kai wuta zuwa garin na Ningi ta koma daga Jihar Jigawa, an yi ta fama da karancinta. Kadan daga cikin bakin mulkin goodluck kenan Allah ya kiyaye gaba!!!
Posted on: Mon, 05 Aug 2013 08:55:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015