ABUN MAMAKI KUMA ABUN HAUSHI DA TAKAICI Wato wannan abin - TopicsExpress



          

ABUN MAMAKI KUMA ABUN HAUSHI DA TAKAICI Wato wannan abin haushin ya faru ne sati dayada tarewar AMARYAR... Wato kawayen amaryar ne suka zo irin ziyaran nan wajen qawarsu tun da ta yi sati daya da aure, bayan sun gaggaisa sai amarya ta shiga Kitchen domin ta girka musu dan abin kalaci... Ashe mijin yana daki kuma yana ganin ta... Tana komawa daki sai angon ya zo ya kashe STOVE din wato RISHON. Bayan dan wani lokaci sai amarya ta dawo kitchen dan ganin ruwan da ta dora ko ya tafasa... Sai ta zo ta ga risho akashe... Abin ya bata mamaki amma duk da haka sai ta kuma kunnawa kana ta koma wajen kawayen ta. Again dai angon ya kuma fakar numfashin ta yazo ya kashe... Haka aka yi har sau uku... A karshe amarya ta fusata ta zunduma uban ashar akan cewa UBAN WAYE YAKE KASHE MIN RISHO...?? Ita ta yi ne ba tare da ta san angon bane... Shi kuma gogan yana ji sai yafito yace UBANKI NE... Amarya abin ya bata mamaki tace kayi hakuri ai ban san kai bane... Yace karya kikeyar iska.. Ki fice min daga gida keda qawayenki na SAKE KI saki UKU! Wai shin anya kuwa akwai SO da KAUNAR JUNA a tsakanin su??? Kawai saboda za a ci ma ABINCI sai ka saki matarka? Admin: #Hafizlaminhassan
Posted on: Sun, 20 Oct 2013 21:43:25 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015