Abul Adfal yana kwance a cikin shagon dinkin abokinsa, - TopicsExpress



          

Abul Adfal yana kwance a cikin shagon dinkin abokinsa, bayan yayi hira ya gaji kamar yadda ya saba in yaso nishadi, kasancewar an riga anyi sallar azahar, yake ganin zai iya dan kishingida kafin la’asar. Hayaniyar da yaran suke a waje yasa ya farka daga gyangyadin daya fara; ya tashi ya nufo su da niyyar ya kore su ko ya samu yayi barci. Matsowarsa kusa yasa ya gane dalilin hayaniyar yaran; wata farar tattabara ce a hannun daya daga cikinsu, yana mai fadin ai ni na fara ganinta. Yaya akai ?Meke faruwa ne? Ya tambayi yaron dake riqe da tattabarar. “wai dan na tsinci tattabara shine suka ce sai na basu, kuma ni na fara ganinta”. To ku tsaya, yanzu yanda za ai ku sayar min da ita, tunda ku hudu ne ga ‘dari biyu sai ku raba naira hamsin-hamsin. Yana karbar tattabarar sai ya wurga ta sama da niyyar ta tashi; amma akasin hakan sai ta fado, yaron ya dubi Abul Adfal yace: “ai bata tashi”, to naji kuje tunda dai na baku kudinku. Abul Adfal ya nisa yana tunanin haqansa bai cimma ruwa ba kenan, dama burinsa ya sake ta, gashi kuma bata tashi, gashi kuma… tunaninsa ya katse lokacin da ya fahimci cewa fiffiken tattabarar na ‘bangaren hagu yafi dayan tudu, hakan yasa yayi saurin ‘daga fiffiken a tunaninsa ko karyewa tayi. Tunaninsa yaa canja ne a lokacin da yaga wata ‘yar qaramar laya a ‘daure a qarqashin fiffiken tattabar, cikin mamaki da al’ajabi yace INNA LILLAAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN, LAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIIYIL AZIIM, A’UUZU BI KALMATILLAHIT TAAAMAATI MIN SHARRI MA KALAQA WA BISMILLAHIRRAHM ANIRRAHIIM, sannan ya sa hannu ya ciro layar. Yana cire layar ya saki tattabar ta tashi abinta, tunanin me hakan yake nufi yasa yayi sauri ya juya ya kira yaron nan ya tambayeshi a inda suka tsinci tattabarar, suka yi masa kwatance sannan ya sallame su suka tafi. Abul Adfal ya warware layar nan kaf, sannan ya ciccire wasu allurai da aka sassoka a jikin wata takarda, sannan ya bude takardar, ‘ZAINAB’ haka aka rubuta a jikin takardar, yaja dogon numfashi sannan ya sa takardar a aljihu na nufi gida dan yayi wankan yamma. Da misalin qarfe biyar na yamma Abul Adfal ya nufi inda yaran nan suka yi masa kwatance, yana zuwa unguwar ya sami wani saurayi ya tambaye shi ko yasan wata Zainab a unguwar, saurayin yace E, amma Zainab din da ya sani yau kusan wata biyu kenan bata da lafiya; yauwa ita nake nufi inji gogan namu, saurayin ya nuna masa gidan shi kuma Abul Adfal yayi masa godiya sannan ya nufi gidan. Da zuwan sa sai ga wata ‘yar qaramar yarinya ‘yar kemanin shekara biyar; sai ya tambayeta “ke menene sunanki? Halima, yarinyar ta amsa, ina yayanki”? (kunji gogan namu da canke, ko yasan tana da yaya oho) Yarinyar ta amsa Yaya Kabir? Yanzun nan ya shiga gida, yauwa je ki kira minshi. Kabir ya fito (saurayi dan kemanin shekara 22) yana kallon Abul Adfal da alamun rashin ganeshi a fuskarsa. Abul Adfal ya gabatar da kansa sannan yayi masa bayanin abinda ya faru game da tattabara, “Dan Allah idan baza ka damu ba muje cikin gida mana?” Kabir yake tambaya, “babu damuwa,” inji jarumin namu. Suna shiga suka tarar da Babar su Zainab da Babansu a falo suna hira. Bayan Abul Adfal ya gaishe su sai Kabir yayi musu bayanin abinda Abul Adfal ya gaya masa. “Ina Zainab din take” Abul Adfal ya tambaya, tana nan cikin dakin dake bayan ka (Babar ta amsa), yau watanta biyu ko magana bata iyayi bare tashi, sai dai akwantar a tayar, munyi maganin asibiti har mun gaji mun barwa Allah sauran… “Yaya Zainab”, Halima ta kira sunan… dukan su suka waiga dan suga wacce ake kiran, Zainab ce a tsaye, jingine a jikin qofar dakin da Abul Adfal yake, daka ganta kaga wacce ta dade tana cuta, duk ta rame, Zainab? Babarta ta kira sunanta cikin mamaki; Zainab ta yi yunqurin ta amsa amma hakan ya gagara kasancewar ta dade batayi magana ba, sanadiyyar hakan yasa ta yanke jiki zata fadi; cikin sauri Abul Adfal da ke kusa da ita yasa hannuwansa biyu ya tare ta, ta fado jikinshi… mu hadu a kashi na biyu.
Posted on: Fri, 22 Nov 2013 08:52:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015