BA A GA WATAN RAMADHANA BA! Kamar yadda mai alfarma sarkin Musulmi - TopicsExpress



          

BA A GA WATAN RAMADHANA BA! Kamar yadda mai alfarma sarkin Musulmi ya bayar da sanarwar duba jinjirin watan Ramadana a yau Litinin! To, Supreme Council For Shari‘a sun fitar da sanarwa cewa: Ba a ga jinjirin watan Ramadana ba, wanda hakan ya sabbaba cikar watan Sha‘aban kwanaki talatin cur, ranar Laraba ta kasance itace ranar da zata zama d‘aya ga watan Ramadana insha Allah. Shikenan dama kwanakin watan Musulunci 29 ko 30 ne. An kar‘bo Hadithi daga Abdullahi ‘Dan Umar (Radhiyallahu Anhuma) yace: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: ((Idan kunga wata (na Ramadana) kuyi Azumi, idan kunga wata (na Shawwal) ku ajiye Azumi, idan kuma ya ‘boyu gare ku (Baku ganshi ba) to, ku cika (Sha‘aban) kwana talathjn)). [Bukhari: 1,906, Muslim: 1,080] ALLAH ya kaimu laraba lafiya, yasa mu fara Azumin cikin Qoshin lafiya da lafiyayyen Imani. (Amee
Posted on: Mon, 08 Jul 2013 22:27:19 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015