BASIRUN BISIRIR GAIBU QABLA KIYANIHI (4) MAI GANI NE DA SIRRIN - TopicsExpress



          

BASIRUN BISIRIR GAIBU QABLA KIYANIHI (4) MAI GANI NE DA SIRRIN GAIBU KAFIN ABIN YA FARU ========================== 11) Daga abu hurairata r a yace Manzon Allah yace na rantse da Allah duniya ba zata tafi ba har sai wani lokaci yazowa mutane, mai yin kisa baisan saboda yayi kisan ba,, wanda kuma aka kashe bai san danme aka kashe shiba,, sai aka ce kamar yaya kenan ya Rasulallah? Sai Annabi ya ce saboda yawan riginrimu, to mai yin kisan da wanda aka kashe duk yan wuta ne,,, musulim ne ya rawaito,, anan ma Annabi ya fito da (gaibu), 12) An kar6o hadisi daga abi musal ashariy r a daga Manzon Allah s a w lokacin da yayiwa sayyadina Abubakar da sayyadina Usman bushara da Aljanna sai kuma yace amma kuma wasu masibu zasu same shi kafin ya mutu,, bukhari da musulim ne suka rawaito. Idan me karatu ya duba sosai zai ga anan Annabi s a w ya bada labari da gaibu cewar wasu masibu zasu sami sayyadina Usmanu, sun kuma same shi,, 13) An kar6o daga ibn Umar r a cewa shi yaji Manzon Allah s a w yana fuskantar mahudar rana yana cewa ku sani hakika fitina tana nan zata 6ullo inda kahon shaidan yake 6ullowa,, bukhari ne yarawaito,,, anan ma Annabi ya bada labari na gaibu akwai fitintinu da zasu 6ullo daga mahudar rana,,, 14) An rawaito cewa yahudawa sunayin atishawa a wurin Manzon Allah s a w dan suna so yace musu Allah yayi musu rahama(to da yake yasan abinda suka kunso a ransu sai yace musu) Allah ya shirye ku, ya gyara zuqatanku,, kaga anan haqiqa wannan hadisin ya nuna cewa Annabi ya san hakan tun kafin ya kasance,,, 15) An kar6o daga abi hurairata r a Manzon Allah s a w ya ce alkiyama ba zata tashi ba har sai wata wuta ta fito daga kasar hijaz ta haskaka wuyayan rakuma yusra,, bukhari ne yarawaito,, 16) An kar6o daga abi hurairata r a ya ce Manzon Allah s a w alkiyama bazata tashi ba har sai musulmi sun yaki yahudawa, su kashe yahudawan har sai bayahude ya 6uya abayan dutse da bishiya, sai dutsen da bishiyar su ce ya musulmi ya bawan Allah ga wani bayahude, a bayana ya 6uya, sai dai bishiyar (farar qaya garkadu) itace bazata fada ba domin ita tana daga bishiyar yahudawa ce,,, musulim ne ya rawaito, idan mai karatu ya duba sosai zaiga cewa duk wadannan abubuwa a wannan zamanin suke ta faruwa amma tini Annabi s a w yabada labarin su to kuwa ai dole ne ace yasan (gaibu),, 17) An kar6o daga ibn Umar r a yace wata rana Annabi s a w yace Allah kayi albarka ga sham da yaman, sai wasu suka ce harda najadu, sai Annanbi s a w yace Allah kayi albarka ga sham da yaman, suka maimaita masa, sai ya ce anan ne za a samu girgiza da fitintinu, kuma anan shaidan zai bayyana,, nanma idan muka duba zamu gani gaibu ne Annabi ya bayyana,, ;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;; wannan shi ne qarshen wannan taqaitaccen littafin Allah yasakawa marucin sa MALAM SHAMWIYLU ADAM GAMA c. Shugaban Qadiriyya ta nassarawa l.g kano,, ALLAH YA QARA MANA SON ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM,, N&K
Posted on: Fri, 15 Nov 2013 01:08:21 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015