***BREAKING NEWS*** BA BOKO HARAM NAN DA WATA 3. - TopicsExpress



          

***BREAKING NEWS*** BA BOKO HARAM NAN DA WATA 3. Inji Jonathan Shugaban NajeriyaGoodluck Jonathan ya shaida ma mutanen Najeriya cewa masalar Boko Haram a nan kasar za’a kau da shi nan da wata uku (3). Jonathan ya bayyana haka ne yayin da ake hira da shi a tashar CNN yace tsarin da matakan tsaro na Najeriya tayi na kokarin ta kau da matsalar ta kungiyar ta Boko Haram. Yace gwamnatin tarayya ba tayi maganar sulhu ba da kungiyar amma ta na neman hanyoyin gyara ma yan kungiyar ta Boko Haram gurin zama, yace ba batun sulhu da Boko Haram kuma ba hakuri ake basu ba. “tsarin tsaron mu an tsara shi ne ayi yaki da ta’addanci amma tunda wannan kungiyar ta fara sai mun ka ci gaba da wannan tsarin. Zan so kuyi hira da ni nan da wata uku game da boko haram ku ma da kan ku za ku yabe ni cewa lalle wannan gwamnatin tayi kokari”. “muna yaki da ta’addanci ko wane bangare, kuma muna so mufara tsayi da su ne ta hanyar sa sojoji sus a mana hannu shiya sa galokacin muka sa dokar-ta- baci ajihohi guda uku inda muka gan cewa ta’addanci ya fi yawa”. Inji shugaba Jonathan. *** DAGA FAGEN NAZARI DA TUNANI ***
Posted on: Mon, 22 Jul 2013 15:15:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics



**

© 2015