BUDURWA KO BAZAWARA 1 MATASHIYAR LABARIN Rana tayi zawwali don - TopicsExpress



          

BUDURWA KO BAZAWARA 1 MATASHIYAR LABARIN Rana tayi zawwali don haka atuni tabaje kolinta inka duba mutane kowa nata kokarin tafiya wurin neman abinci.Karfe goma daminti ashirin da biyu ,amma jinake kamar karfe daya na rana ,sabili da yanayin bazara damuke ciki Ina tsaye abakin titi daidai envestment house, hakika innacema ga inda zani to nayi karya .Zuciyata cike take ta tunani dakuma takaicin wulakancin da sakinat tayimi yau kwanana uku rabon da insata a idanuna Nayi qyacci gami da ajiyar zuciya, wai ni sakinat zatama haka ko NA TAMBAYI KAINA ,SABODA TAsamu wanda yafini. wai har tanacemu ita yanzu basa atabace in inason inyi soyayya da ita to maza inje innemi Qiri ita tawuce ajin talasko .tamanta irin so da kaunar danake mata .kusan shekarmu uku da ita muna soyayya amma dare daya wai yarinyar nan zata juyamun baya. Hmmn nayi ajiyar zuciya gami da fadi afili wlh tallahi indai inada rabon arziki se nasamu Qirin da sakina TAke cewa inje innema. ALokaci guda kuma tunanina yakoma can farkon rayuwata. Natuna sanda mahaifina yake min nasiha sauhel wlh kayi kokari kadage da karatu don bamuda wani abu wanda zamu barmuku inaba ilmiba inkanada ilminka ko ina kaje zaka iya dogaro da kanka domin ilmin nan shine gishirin zan duniya Na tunano lokacin da nakare secondry sch inata kokarin fafutukar neman aikin soja amma saboda ba hanya da kuma abinda ya hadamu da masoyiyata wato QIRI HAkan be samuba Natuno farkon haduwarmu da sakinat da kuma irin soyayyar damukai da ita amma wai yanzu lokaci daya zata juyamun baya saboda ta samu wanda yafini abin hannu. lokaci daya kuma tunanina ya juya wurin hudubar uban gidana danike ma leburanci kwalli me gini .wata rana muna aikin gini yake cemun sauhel kayi kokari ka koyi sana a ko tanan zaka iya dogaro da kanaka kaga misali ni banyi karatun boko ba amma kaga inda allah ya aje abincina dashi nake cida gidana har intaimaki iyayena........... Tunanina ya katse lokacin da naji hon din mashin kusa dani se alokacinne hankalina yadawo jikina na duba inda akai hon din fuskar da nashekara uku akalla ban ganiba ita nayi arba da ita, umma ne abokina da muka gama secondry sch tare. yau akalla she karata uku kenan ance yana abuja yana kasuwanci. BABAAA nace don haka muke cemai .ya akai naganka tsaye wuri guda kuma gefen babban titi kana ta tunani?lafiya kuwa yakara tambayata? hmmn kaidai kabari kawai zanbaka labari..... 12/7/ 2005 ABUJA NAJERIA FARKON HADUWATA DA ITA Duk tituna takwas dinda suke kan juction din AYA dake asokoro cike suke da go slow sakamakon tasowa aikin da akayi dakuma hadarin dake kokarin tasowa ,kowa na kokarin yakai gida kar ruwa yaritsashi. tsakiyar traffic din gakuma wata tirelan mai ta makale atsakiyar hanya wannan yasa komai yatsaya cak atitunan don bawata mota dake iya matsawa gaba balle baya inkadaga kanka ba abinda da kake hange acikin goslow se masu tallan kayayyaki kala kala. SAnye nike da wando tree queter da matsatsyiyar riga boddy hop ajikina kafata sanye cikin takalma kunfu dauke nike dawata tafkekiyar leda me kama da ta buhun madara wani karamin katako ne akashinfida acikinta aka jera lacasera juice viju milk kusan catton katton na fasa kankara asman kayan kayan sun dau sanyi abin gwanin ban sha awa............... zamuci gaba gobe war haka in Allah ya kaimu kayi like in labarin zeayima dadi yawan like dinku shike karamana kwarin gwiwa ABBAN MUSADDIQ
Posted on: Fri, 02 Aug 2013 19:58:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015